Umar Faruk Birnin-kebbi" />

Covid 19: Gwamnatin Kebbi Ta Samar Da Na’urorin Numfashi Biyu A Cibiyar Killace Masu Cutar  

Gwamnatin Jihar Kebbi ta samar da na’uar taimaka wa marasa lafiya da nunfashi guda biyu a dakin ICU Santa da ke a cikin Asibitin Tunawa da Sarki Yahaya da ke a Birnin-Kebbi a jiya.

 

Bayanin hakan ya fito ne daga bakin Kwamishinan ma’aikatar Kiyon Lafiya, Alhaji Muhammad Jafaru kuma Shugaban Kwamitin Taskforce kan Kwarona a jihar ta Kebbi yayin da ya kira taron manema labaru a jiya, don bayyana wa ‘yan jaridu kan irin ci gaba da daukar matakan da gwamnatin jihar ke yi na shirin kar ta kwana game da ballar cutar kwaronabairus a kasa Nijeriya don gudun barkewar cutar  a jihar ta Kebbi. Wanda Allah ya kare har yanzu nan dai ba a samu ballar cutar ba.

 

Haka kuma ya ce “wadannan na’urorin na taimawa mai dauke da cutar coronabirus da bai iya nunfashi da kyau ko kuma marasa Lafiya wanda ke bukatar taimako kan nunfashi su ne ke bukatar na’urar”.

 

Saboda haka, gwamnatin jihar Kebbi a karkashin jagorancin Gwamna Abubakar Atiku Bagudu tana kan daukar matakai wurin ganin cewar ba a samu barkewar ko ballar cutar a duk fadin jihar ba.

 

Haka zalika Kwamishinan ya yi kira ga al’umma a duk fadin jihar da su ci gaba da bin umurnin da kuma dokokin da aka sanya don kariyar kansu da kuma lafiyarmu musamman rage yawan haduwar wuri guda da kuma tabbatar da yawan wankin hannuwa da hand sanitizer da kuma kasance wa a gida har zuwa wani dan lokaci .

 

Daga nan ya ce “gwamnatin jihar Kebbi ba ta tsaya nan ba kawai tana ci gaba da fadakarwar da kuma yekuwa kan abubuwan da jama’a ya kamata su rika yawan aiyanawa don kariya ga kamuwa ga cutar coronabirus”.

 

Daga karshe ya gode wa dukkan al’ummar jihar kan irin goyon bayan da suke bayar wa da kuma irin namijin kokarin da matakai da Gwamna Abubakar Atiku Bagudu ke dauka don tabbatar da cewar jiharsa ba ta samu barkewar ko ballar cutar coronabirus ba, saboda hakan muna godiya kwarai da gaske.

Exit mobile version