Umar Faruk" />

COVID-19: Irin Matakan Da Gwamnatin Kebbi Take Dauka

Gwamnatin Jihar Kebbi ta ci gaba da daukar matakai na ba da kariya ga al’ummar ta a fadin jihar baki daya.

Matakan da ta riga ta dauka sun hada da fadakarwa da yekuwa ta yadda za a tsaftace muhalli da kuma na jiki musamman wanke hunnuwa da nisanta daga wanda ke tari ko yawan zafin jiki da sauransu. Haka kuma an dauki Matakin horas da matan shuwagabannin kananan hukumomi, kwamishinoni da na ‘yan majalisar dokoki na jihar kan yada za a wanke hunnuwa don ba da kariya ga dauka ko barkewar cutar a cikin kananan hukumomin da kewayen su.

Haka kuma Gwamnatin Jihar ta kafa Kwamitin jami’an kiyon lafiya don ba da agajin gaggawa kan wanda duk aka samu yana dauke da cutar ta coronabirus a jihar.

Har ilayau bata tsaya nan ba kawai, ta koma kafa wani Kwamitin da ke sanya ido da kuma daukar matakin na gaggawa idon an samu wani ko wata da alamomin da ake tuhumar cewar yana dauke da cutar coronabirus domin daukar  matakan gaggawa ba tare da bata lokaci ba wato (Kebbi State Taskforce Team) wanda Kwamishinan ma’aikatar Kiyon Lafiya na jihar Kebbi, Alhaji Muhammad Jafaru ke jagoranta sai Babban Sakataren ma’aikatar ta Kiyon Lafiya, Alhaji Hassan Mai-Gundi zai kasance a matsayin Sakataren Kwamitin.  Haka kuma an yi tanadin wuraren da za a killace duk wanda aka sama na dauke da cutar a dukkan Asibitotin na kananan hukumomin jihar gudu 21.

Haka zalika gwamnatin jihar Kebbi ta dauki matakin rufe dukkan makarantun firamare dana sakandare kai har ma da masu zaman kansu a duk fadin jihar ta Kebbi don rage yawan haduwar Jama’a wuri daya.

Bugu da kari dukkan ma’aikatun gwamnatin jihar an bada sanarwar rufe su, amma dai akwai wasu nau’in ma’aikatu da wannan umurnin bai shafe su ba .

Kamar hukumar tattara haraji, ma’aikatar kudi, hukumar samar da ruwan sha da kuma jami’an tsaro. Sauran sun hada da Kafafen yada labaru da kuma ma’aikatar Kiyon Lafiya da jami’an ta da kuma wasu dadarkun mutane wadanda keyi wa Gwamna da fadar gwamnatin hidima.

Duk wannan wani mataki ne na rage yawan haduwar Jama’a don gudun barkewar cutar ta coronabirus a cikin jihar ta Kebbi.

Haka kuma dukkan matafiyan da za su shigo jihar ta filin jirgi ko ta iyakokin jihar, jami’an kiyon lafiya  za su gudanar da bincike kan yanayin lafiyarsu kafin a barsu su shigo cikin jihar ko kuma kafin su fita.

Hazalika Gwamnan jihar, Abubakar Atiku Bagudu tuni dai ya killace kansa da kuma iyalansa daga haduwa da jama’a a cikin jihar.

Har ilayau masarautar Gwandu ba a barta a baya ba, ita ma ta gudanar da taron tattaunawa da kuma fadakar wa ga dukkannin sarakunan ta na gargaji a duk fadin masarautar don fadakar dasu irin matakan da za su dauka da kuma sanar da Jama’ar su na yankunan da suke jagoranta don su iya kare kansu ga kamuwa ga cutar. Musamman yadda a ke wankin hunnuwa da kuma rage yawan haduwar jama’a wuri daya .

Kawo yanzu dai ba a samu barkewar cutar coronabirus a jihar ta Kebbi ba, amma dai gwamnatin da jama’ar ta na kan daukar matakai don ganin cewar ba a samu barkewar cutar ba.

Su ma jama’ar cikin garin Birnin-Kebbi da yawan su sun killace kansu ga yawan haduwar wuri guda domin idon ka fito a manyan titunan cikin garin na Birnin-Kebbi za ka gan manyan titunan babu yawan mutane wanda sun yin hakan ne don bin umurnin da kuma dokar da jami’an kiwon lafiya na jihar suka sanar don kariya ga kamuwa da cutar.

Exit mobile version