Ibrahim Muhammad" />

COVID-19: Kar Mu Yarda A Raba Mu Da Imaninmu – Wakilin Dukiya

An bayyana cewa annoba ta saba faruwa a fadin duniya a karni daban-daban har zuwa yau, idan ta zo sharia ta yarda kar a shiga gari kar a fita,to amma yakamata musulmi musulmi a kiyayi yaza zantuka na babu gaira babu dalilinsa.Wani dan kasuwa a jihar Kano, Alhaji Yusuf Ibrahim Wakilin Dukiya ya bayyana hakan a tattauwarsa da manema labarai.

Ya kara da cewa, a matsayimmu na musulmi, Annabi ya yi mana hani da surutai barkatai ya yi umurni akan mu kame harshenmu. Amma yanzu harsuna na surutai barkatai sun yi yawa kuma anata yada abubuwa da basu da amfani.
Alhaji Yasuf Ibrahin ya yi nuni da cewa, annoba gaskiya ce amma a zahiri a halin da ake ciki abin na nema ya cimma addininmu mu shiga cikin wani hali wanda ya isa mu roke shi kuma muna bijire masa ta kawo son rai da tsari irinna na turawa ana nema a koma a rika yarda da maganarsu wannan abin neman tsari ne domin duk annoba Annabi ya gaya mana maganinta tayin addu’a da neman gafarar Ubangiji mu tuba gare shi ko ruwan sama aka rasa annoba ne muna tuba gare shi yana shayar damu, haka kwalara annoba ce.
Ya ce, saboda murar mashako irinta turawa sai mu zo mu dauka gaba daya muce baza mu yi addininmu ba, ba zamu shuga mu yi Sallah ba. “Wa’iyazu Billahi bama daga cikin wannan tsari na turawa na duniya. Dukkanmu dasu abokan mu’amala ne amma ba za mu yarda addininmu ya tabu ba. Kada mu yarda addininmu ya tabu azo a cimma musulunci yakamata mutane mu koma ga Allah da addu’oi da tuba akan ya yaye wannan masifa”
Ya kuma ce, kashe-kashe da ake bai sa an tada hankali ba sai wannan annoba, anata kashe mutane anan da can kowa yaki magana amma an wayi gari abu kankani bai kai ya kawo na abinda aka kashe ba anzo anata neman juyar da imanin mutane.Yakamata tun da ‘yan Nijeriya mu yi ta fatan Allah ya kiyaye mu daga wannan annoba ta kusantar Ubangiji.
Alhaji Yusuf Ibrahim Wakilin Dukiya ya ce, yanzu takai wanda bai inganta imaninsa ba takai yana ganin yin musabiha wai zai dauki cuta kuma bayan haka ana gujewa addini ta wajen haduwa a yi Sallah. Wannan yayata wannan annoba da ake kururuwa ce ta shaidan domin Yahudawa har abada ba za su bari a zauna lafiya ba, ya zama wajibi mutane su fahimci haka su kusanci malamai su fada musu gaisuwa. Mutane su kama neman gafara da rokon Allah. A daina jin abu ana yayatawa don a tashi hankalin al’umma a fawwalawa Allah komai shi zai yaye duk wata annoba.

Exit mobile version