Connect with us

RIGAR 'YANCI

COVID-19: KEDCO Ta Bada Tallafin Kayan Abinci Ga Gwamnatin Kebbi

Published

on

A jiya ne kamfanin samar da wutar lantarki da ke Kaduna wato (Kaduna Electric Distribution Company) ta bada tallafin kayan abinci ga gwamnatin jihar Kebbi don rabawa talakawan jihar don rage radadin matsalar da aka shiga na bullar coronabirus a mafi yawan jahohin kasar Nijeriya .

Kayan Abinci dai sun hada da Buhu 500 na shinkafa, katon 400 na makaroni, katon 100 na man dafa abinci da kuma Buhu 100 na Samonbita don rabawa talakawan da kuma mabukata ‘yar jihar ta Kebbi. An gabatar da kayan tallafin abincin ne a Birnin-kebbi a jiya.

Da yake gabatar da tallafin kayan abincin ga gwamnatin jihar ta Kebbi, shugaban kamfanin da ke da Babban mazaunin ofishinta a Kaduna, Injiniya Garba Haruna wanda ya samu wakilcin shugaban kula da sashen gudanar da ayyukkan kamfanin na yau da kullun a Jahohin Sakkwato, Kebbi da kuma Zamfara, Mista Sunday Yahaya, inda ya samu rakiyar wasu manyan ma’aikatan kamfanin kamar shugaban mai kula da sashen yada labaru na kamfanin Malam Idris Muhammad, Manajan ofishin kamfanin a shiyar Kebbi ta Arewa Abdulwahab Suleiman don gabatar da kayan abincin ga gwamnatin jihar ta Kebbi a jiya .

Shugaban kamfanin dai ya ce ” wannan tallafin kayan abincin da kamfanin ya bayar don rabawa talakawan jihar ta Kebbi na daya daga cikin aikin muna tallafawa al’ummar da muke huldar kasuwanci dasu da kuma ita kanta gwamnatin wanda shine a kira a turance (corporate social responsibility) da muke yi a duk lakocin da bukatar yin hakan ta taso a duk fadin jahohin da muke da ofishi”.

Injiniya Garba Haruna ya kara da cewa ” kamfanin KEDCO a shirye muke na tabbatar da cewar mun sauke nauyin da ya rataya akan mu zuwa ga al’ummar kasar nan”.

Daga karshe ya bayyana jindadinsa da kuma godiyarsa ga gwamnatin jihar Kebbi da kuma jama’ar ta Kan irin hadin kan da ake basu wurin gudanar da ayyukkansu a jihar .

Tallafin Kayan Abinci dai an hannun ta shine a hannun Kwamitin coronabirus na jihar ta Kebbi a karkashin jagorancin Kwamishinan ma’aikatar Kiyon Lafiya Jafaru Muhammad tare da sauran wasu Mambobin Kwamitin amadadin gwamnatin jihar ta Kebbi.

Yayin da yake karbar kayan tallafin na abinci da kamfanin samar da wutar lantarki na Kaduna ya gabatar shugaban Kwamitin coronabirus na jihar Kebbi Muhammad Jafaru ya godewa hukumar kamfanin samar da wutar lantarki na Kaduna kan irin gudumawar kayan abinci da suka bayar a matsayin nasu tallafin ga al’ummar jihar . Kwamishinan ya kuma basu tabbacin raba kayan abincin ga talakawan da suka dace su cigajiyar.

Haka kuma yayi kira ga sauran kamfunan kasar nan da suyi koyi da kamfanin samar da wutar lantarki na Kaduna ga tallafawa al’ummar kasar nan don ganin irin halin da kasar nan take ciki.

Har ilayau shugaban Kwamitin coronabirus na jihar , ya ce ” wannan tallafin kayan abincin da kamfanin samar da wutar lantarki na Kaduna ya bayar ga al’ummar jihar ta Kebbi ya nuna cewar suna sauke nauyin da ya rataya akan su da ake kira a turance (Corporate social responsibility) da kuma nuna irin kyakyawar fahimta da ke akwai tsakanin kamfanin da kuma gwamnatin jihar ta Kebbi”.

Daga nan shugaban Kwamitin coronabirus na jihar ya ce ” amadadin gwamnatin jihar Kebbi da kuma jama’ar ta muna godiya kwarai da gaske ga irin tallafin kayan abincin da kamfanin KEDCO ya kawo a jihar don rabawa al’ummar jihar . Saboda gwamnatin jihar Kebbi tana kira ga jama’ar ta nasu ci gaba da baiwa kamfanin KEDCO hadin kai da kuma goyon baya wurin tabbatar da sun gudanar da ayyukkansu na samar da wutar lantarki a cikin jihar batare da wata matsala ba . Bisa muna kara nuna godiyar mu”.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: