Abdulrazaq Yahuza Jere" />

COVID-19: Kungiyar Ci Gaban Funtuwa Ta Tallafa Wa Kimanin Magidanta 100 Da Naira 15,000

Shugaban Kungiyar Tabbatar da Ci gaban Yankin Funtuwa da ke Jihar Katsina, a Shiyyar Abuja, Hon. Ibrahim Lawal Usamah ya bayyana cewa kungiyar ta tallafa wa sama da mutum 100 da Naira dubu 15,000 kowanne domin saukaka musu radadin halin da ake ciki na zaman gida saboda annobar cutar COVID-19.

Ya bayyana haka ne a zantawarsa da wakilinmu ranar Asabar, inda ya yi bayanin cewa akwai bukatar ‘yan kasa su taimaki junansu a wannan lokaci na jarbata da ake ciki.

“Mun kirkiri wannan kungiya ce don taimakon al’umma, bisa lura da wannan yanayi da Allah ya kawo mu muke ciki wanda duniya ta rude ta shiga fitina da tashin hankali na wannan cuta ta COVID-19. Mafi yawanci gwamnatoci sun ba da umurnnin kowa ya zauna gida a matakin tarayya da kuma jihohi, inda abin zai kasance ba shiga ba fita. Lura da wannan muka ga cewa akwai mutane da yawa a Nijeriya wadanda sai sun fita nema ne sannan za su iya ciyar da iyalansu, idan aka ce su zauna gida to ka ga an kara samun cuta ta biyu kenan da za ta yi kisa, ita ce yunwa.

“A karkashin wannan, ya kamata kowane dan kasa ya bayar da gudunmawar da zai iya badawa tun da har yanzu ba mu ji wata ko wani mutum guda daya da ya fito ya ce ga tasa gudunmawa domin wannan aiki ba na saukaka wa jama’a radadin zaman gida, shi ne muka ga mu ya kamata mu yi kokari ubanen kungiyarmu da mambobinmu da talakawan da ke gefenmu, mu ga me za mu iya yi musu. A karkashin wannan a matsayina na shugaban kungiya na ba da umurni iyayen kungiya kowane a ba shi Naira 20,000 domin ya sayi buhun shinkafa ya dan yi hidimar ciyar da iyali. Sauran mambobi kuma kowane a ba shi Naira 15,000 wanda akalla sama da mutum 100 ne za su ci gajiyar wannan abin in sha Allahu. Kuma an aiwatar da wannan, da yawa kowane ya ji sako a cikin asusun ajiyarsa na banki,” ya bayyana.

Hon. Ibrahim Lawal Usamah ya kuma jinjina wa ‘ya’yan kungiyar bisa hadin kai da goyon bayan da suke bayarwa don samun nasarar ayyukan da suke yi.

“Ina kara mika godiya ga ‘yan kungiyar nan. Tun da muka kirkire ta akwai wadanda ma ban san su ba amma muna tafiyar da komai cikin hadin kai. Kuma duk wani abu da za a bayar na amfanin jama’a mutum yana zaune zai samu ba sai ya yi dogon mika ko shan wahala ba. Gwamnati ya kamata a ce tana da irin wannan tsari na taimaka wa al’ummarta”.

Hon. Ibrahim Usman ya kuma shawarci ‘yan kungiyar game da bin matakan samun kariya da riga-kafin kamuwa da wannan cutar, inda ya yi musu albishir da samun kulawar likitocin da suka tanadar musu a duk lokacin da bukatar hakan ta taso.

“Duk wanda yake karkashin wannan kungiya idan ya ji wani yanayi a jikinsa da bai gane ba, akwai likitoci da muka tanada na musamman wanda za mu bayar da lambobinsu ba da jimawa ba wadanda da ka kira za su zo su same ka; su duba ka don ba ka gudunmawar da kake bukata,” in ji shi.

To shin ko a ina ita wannan kungiyar take samun kudin shiga ganin irin hidindimun da take gudanarwa masu dan nauyi? Hon. Ibrahim Lawal Usamah ya bayar da amsa, inda ya ce, “e, lallai akwai wadanda suke tambaya wai shin a ina ne muke samun kudin shiga na aiwatar da wadannan abubuwa. To, da farko dai ita wannan kungiya mai girma Gwamnan Katsina, Alhaji Aminu Bello Masari ya kaddamar da ita a gidan gwamnatin Katsina da ke nan Abuja kuma ya yi alkawarin cewa zai neme mu akwai gudunmawar da zai bayar, amma na san saboda abubuwa sun yi masa yawa har yanzu dai ba mu samu muka tattauna da shi ba. Sannan akwai Hon. Mukhtar Dandutse shi ne wanda ya ba mu Kekunan Napep kuma kasancewar a lokacin da ya ba mu; ba mu da asusun ajiya na banki, duk kudaden da ake samu da kekunan a cikin asusunsa muke zubawa wanda har yanzu abubuwa sun mai yawa shi ma ba mu samu damar ganin sa domin lissafa kudaden tare da amsa ba. Saboda haka mutanenmu da muke tare da su na arziki tun daga kan Sanatocinmu da ‘Yan Majalisar Wakilai galibi su suke tallafa wa wannan kungiya,” in ji shi.

Hon. Lawal ya kuma bayyana cewa ba su nuna wariya yayin da suke rabon, yana mai cewa, “Dukkan Dan Adam mai rai ai abin tausaya wa ne. Ba mu nuna wariya, mutanen yankin Funtuwa daidai gwargwadoniya karfinmu suna cin gajiyar abubuwan da kungiyar nan ke yi. Sannan wani abin farin ciki shi ne daga cikin wadanda suke fara ganin sakon wannan kungiya shi ne mai girma Sarkin Maska, Hakimin Funtuwa da kuma lmamai namu na Masallatan Izala da Darika wanda da su muka bude bayar da wannan tallafi sannan a ci gaba da bai wa mutane.”

Wannan yunkuri na Kungiyar Tabbatar da Ci Gaban Yankin Funtuwa a Shiyyar Abuja abin koyi ne ga sauran takwarorinta domin saukaka irin halin da marasa karfi da ke cikin al’umma za su iya tsintar kansu a ciki saboda kullen da aka yi musu a gida tare da iyalansu ba kuma tare da wani tanadin kirki na abincin da za su ci ba.

Exit mobile version