Connect with us

DAGA BIRNIN SIN

COVID-19: Murna Na Kokarin Komawa Ciki

Published

on

A yayin da harkokin cinikayya da zuba jari da sauran fannoni ke dawo wa sannu a hankali a sassa daban-daban na duniya, wadanda a baya suka dakata sakamakon bullar annobar COVID-19, sai ga shi murna na kokarin komawa ciki, yayin da Mashawarci kan zamantakewa da tattalin arziki a kungiyar tarayyar Afirka (AU) da hukumar MDD mai kula da tattalin arzikin Afirka (ECA) Constantinos Bt Costantinos, ya bayyana fargaba kan yadda ake samun karuwar sabbin masu kamuwa da COVID-19 a nahiyar Afirka.

Jami’in ya ce, yadda sabbin masu kamuwa da cutar ke bazuwa cikin sauri, abin damuwa ne matuka, duba da yadda wasu kasashen nahiyar ke zama wuraren da aka fi samun yawan sabbin masu kamuwa da cutar ta COVID-19.

Sai dai duk da wannan matsala, hanya dilo ta cimma nasarar ganin bayan wannan annoba, ita ce hadin gwiwar kasa da kasa da taimakon juna, kamar yadda a kwanakin baya kasar Sin ta kira taron hadin gwiwa don yaki da COVID-19 ta kafar bidiyo. Muddin muka gaza magance wannan annoba a Afirka, hakika za ta addabi duniya baki daya.

A farkon wannan shekara ce, hukumomin yawon shakatawa na kasa da kasa, suka yi hasashen samun ci gaba a harkar yawon bude ido a sassan nahiyar Afirka, suna masu fatan baki daga kasashen duniya daban daban, za su kara kai ziyara irin wadannan wurare dake nahiyar, da karuwar da ta kai kaso 3 zuwa 5 bisa dari a shekara guda.

To sai dai kuma, bullar cutar COVID-19, ta tilasawa kasashen Afirka da dama, abin da malam bahaushe ke cewa, dole kanwar naki, wato aiwatar da matakai masu tsauri na kandagarkin cutar, kuma har zuwa yanzu, jiragen saman kasa da kasa da dama, ba sa gudanar da sufurin fasinjoji, a daya bangaren kuma, kasashe da yawa na aiwatar da dokar kulle, baya ga rufe birane da dama, lamarin da ya sa harkar yawon bude ido tsayawa cak. Sai dai aka ce Komai ya yi Zafi, maganinsa Allah.

Kididdiga ta nuna cewa, yawan mutanen dake aiki a fannin yawon bude ido a kasashe irinsu Kenya, da Afirka ta kudu, da Tanzania da sauran wasu kasashen nahiyar, ya kai mutum miliyan daya. Amma sakamakon bullar wannan annoba, ya sa masu otel-otel, da wuraren cin abinci, da na yawon bude ido sun fuskanci babbar hasara. Ai dama, Ba kullum ake kwana a Gado ba.

Har yanzu dai ba a san ko yaushe ne kasashen Afirka za su sake bude kofofin su ba, ta yadda za a sake komawa hada hadar yawon bude ido ba. Ana cikin wannan fargaba kuma, sai ga shi hukumar cinikayya ta duniya WTO, ta ce yawan cinikayyar kayayyaki a duniya zai ragu da kaso 18.5 a rubu’i na biyu na bana sakamakon COVID-19. Sai dai hukumar ta ce matakan da gwamnatoci suka dauka na tunkarar cutar, sun taimaka wajen rage tasirinta. Wai ana kukan Targade sai ga Karaya.

A halin da ake ciki yanzu, filayen jiragen saman nahiyar na gudanar da jigilar fisinjojin dake komawa gida, da dakon kayayyaki ne kadai, yayin da mafi yawan masu jigilar fasinjoji suka dakatar da ayyukan su.

A cewar kungiyar yawon shakatawa ta duniya, akwai alamu dake nuna cewa, za a iya kaiwa watanni 10 masu zuwa ko fiye, kafin fannin yawon shakatawa na Afirka ya sake farfadowa daga tasirin barkewar wannan annoba. Mai hakuri aka ce ya kan dafa Dutse har ma ya sha Romonsa. (Ibrahim Yaya)

Masana a fannin na ganin cewa, tun da dai sashen ba zai farfado cikin sauri ba, ko shakka ba bu yana bukatar tallafin gwamnati, da ma sauran sassa masu nasaba da shi, kamar na amfani da na’urorin zamani a fannin sufuri, da neman masaukai, wadanda za su karfafa gwiwar masu yawon shakatawa, ta yadda daga bisani, sashen zai farfado kamar yadda yake a baya. Koda yake ba a Bari a kwashe a dai-dai.

(Ibrahim Yaya)

 
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: