Khalid Idris Doya" />

COVID-19: Musabaha Da Dan Atiku Ta Jaza Wa Gwamnan Bauchi

•A Killace Shi Tare Da Mutum 10

•Za Mu Samu Sakamakon Gwaji Cikin Awa 24 – Kwamishinan Lafiya

Gwamnnan jihar Bauchi Sanata Bala Muhammad tare da ‘yan rakiyarsa a tafiyan baya-bayan nan da suka yi sun killace kansu biyo bayan rahoton da ke tabbatar da cewar dan Atiku Abububakar wato Muhammad Atiku na dauke da cutar Coronabairus, inda shi kuma gwamnan ya gaisa da shi a cikin jirgi a tsakanin Legas zuwa Abuja bayan dawowarsu daga tafiya.

A cikin wata kwafin sanarwar manema labaru da Kakakin Gwaman jihar Muktar Gidado ya fitar a jiya Litinin, ya shaida cewar Gwamnan ya dauki matakin ne bayan samun rahoton kamu da cutar da dan Atiku ya yi wanda shi kuma ga gaisa da shi kuma sun yi mu’amala a lokacin da dukkaninsu suka dawo daga kasashen waje kwanakin baya.

Ya ce, bayan samun rahoton da ke cewa dan Atiku, Muhammad Atiku Abubakar na dauke da cutar Coronabirus wanda hukumar dakile yaduwar cututtuka ta kasa NCDC ta tabbatar biyo bayan dawowa da yayi daga kasar waje ta jihar Legas.

Sanarwar ta ce; “Idan za ku iya tunawa, Gwamna Bala Muhammad a kwana-kwanan nan ne  ya dawo Nijeriya daga wata ziyarar aiki da ya kai kasar waje ta jihar Legas, sun hadu da Mohammed Atiku Abubakar a cikin Aero Contractors Aircraft inda suka yi musayar musabaha da gaisuwa.

“Kawo yanzu dai babu wata alamar cutar da ta bayyana a jikin gwamnan, amma a bisa shawarar hukumar dakile yaduwar cututtuka ta kasa, zai ci gaba da kasancewa a killace domin kare yaduwar cutar,” A cewar sanarwar.

Muktar Gidado ya kara da cewa yanzu haka an dibi jinin gwamnan domin yin gwaji a kai da kokarin gano halin matakin lafiyarsa, inda ya ce har kafin zuwan sakamakon gwajin jinin zai ci gaba da kasancewa a killace.

Daga bisani sanarwar ta shaida cewar gwamnan ya dakatar da dukkanin aiyukan da suke gabansa nan ta ke domin kariya da kiyayewa.

Da ya ke karin haske kan lamarin wa manema labaru, kwamishinan lafiya na jihar Bauchi, Dakta Aliyu Maigoro ya shaida cewar cikin awa 24 za a samu sakamakon gwajin jinin gwamnan da a ka dauka domin tabbatar da matakin lafiyarsa.

Kan wadanda gwamnan ya yi mu’amala da su kuwa, kwamishinan yayi bayanin cewar babu wani firgici da su ke ciki a sakamakon gwamna na amfani da sinadarin wanke hannu a kowani lokaci, ya kuma kara da cewa babu wani alami ko kusa da ke bayyana cutar Corona a jikin gwamnan, illa dai an bi umurnin jami’an lafiya ne wajen killace kansa domin tabbatar da kiwon lafiya.

Dakta Aliyu Maigoro, ya kuma shaida cewar yanzu haka jihar ba ta kes din Corona ko guda daya a jihar.

Maigoro ya kara da cewa, gwamnan da iyalansa hadi da ‘yan tawagarsa da su ka ziyarci jihar Legas kwanan baya bayan dawowarsu daga kasar Jamani dukka suna killace, domin tabbatar da kiwon lafiyarsu da na jama’a hadi da samun tabbaci kan makomar lafiyar kowa.

Kwamishinan lafiyar ya jaddada ya nanata bukatar jama’a da su kara rungumar dabi’ar wanke hannu da kula da tsaftar su a kowani lokaci domin tabbatar da yin rigakafi ga cutar ta Corona mai hanzarin kisa.

Kan batun zazzabin Lassa da jihar ke fama da shi kuwa, Kwamishinan ya shaida cewar gwamnatin jihar ta yi kokarinta wajen tabbatar da cewar an kawo karshen matsalar, yana mai fadin cewar kawo yanzu sun cimma nasarori da daman gaske wajen rage kaifin cutar a fadin jihar.

Ya ma kara da cewa yanzu haka kananan hukumomi biyu ne kawai aka tabbatar da barkewar cutar ta zazzabin Lassa wanda suke kan kokarin kawo karshen shi kawo yau.

Batun killace kan gwamnan jihar Bauchi dai shi ne babban lamarin da ke yawo a fadin jihar tun lokacin da sanarwar hakan ya bazu, inda jama’a ke addu’ar kawo karshen cutar da kuma fatan cewar gwamnan bai kamu da ita ba, suna masu fargabar cewar gwamnan shi da kansa yayi mu’amala da mutane da dama ciki kuwa har da malamai da sarakuna, kodayake kwamishinan lafiya a jihar ya nuna hakan a matsayin matakin da babu wani firgici ko tashin hankali a kai, sai ya nemi jama’a da su kwantar da hankulansu.

Exit mobile version