Khalid Idris Doya" />

COVID 19: Mutum Hudu Ake Tsammanin Na Dauke Da Ita A Gombe

Kwamishinan lafiya na jihar Gombe, Muhammad Ahmad Gana, ya tabbatar da cewar samfurin mutum hudu da aka dauka da ake zargin ko suna dauke da cutar Coronavirus biyo bayan mu’amala da suka yi da gwamnan jihar Bauchi Bala Muhammad da ke dauke da cutar ta COVID 19 an gwada su basu dauke da cutar.

Dakta Gana ya tabbatar da hakan ne wa jaridar SUN a ranar Asabar, inda ya kara da cewa dukkanin kesa-kesai hudu da aka yi zargin sakamakon gwajinsu ya fito basu dauke da cutar sam-sam.
A dai ranar Laraba ne kwamitin dakile yaduwar cutar a jihar ta baiwa mutum hudun shawarar su killace kansu bayan da suka yi mu’amala da gwamnan jihar Bauchi har zuwa lokacin a sakamakon gwajinsu zai fito, inda daga bisani aka tabbatar basu dauke da cutar.
Daga bisani dai an samu tabbacin cewar cutar bata jikinsu wanda aka samu tabbacin hakan daga hukumomin da lamarin ya shafa.
Har-ila-yau, gwamnatin ta ce duk da har zuwa yanzu ba a samu mai dauke da cutar a jihar ba, za su ci gaba da zurfafa dauman matakai domin tabbatar da dakile yaduwar cutar da ganin cutar ba ta zo jihar ba.
A shekaran jiya ne dai gwamnan jihar Inuwa Yahaya ya sanar da daukar matakin gwamnatin jihar na kulle dukkanin mashigar jihar, inda kuma ya nemi a rage zirga-zirga tare da dakatar da dukkanin tarukan jama’a domin daukan matakai na kariya.
Da yake ganawa da ‘yan jarida bayan fitowa daga taron ganawa a ranar Juma’a, kwamishinan ‘yan sandan jihar Bello Makwashi, ya shaida cewar hukumomin tsaro an basu umarnin su tabbatar jama’a sun bi dukkanin matakan da gwamnatin jihar ta dauka.
Ya ce, sun kaddamar da kwamiti na sintiri da bibiya domin tabbatar da jama’a suna bin umarnin da gwamnatin jihar ta gindaya mu su.

Exit mobile version