Umar A Hunkuyi" />

COVID-19: Nijeriya Da Wasu kasashe Za Su Yi Asarar Dala Bilyan 65

Nijeriya da sauran kasashen Afrika masu arzikin man fetur za su yi asarar kudaden shigan da suke samu daga cinikin danyan man fetur a sabili da barkewar cutar Coronabirus, hukumar kula da tattalin arzikin kasashen Afrika ce ta bayyana hakan a ranar Talata.

Dangane da Nijeriya musamman, hukumar ta ce barkewar cutar ta COVID-19, zai rage yawan danyan man da take fitarwa a shekara da kimanin tsakanin cinikin dala bilyan 14 zuwa dala bilyan 19.
Hukumar ta yi gargadin cewa matsalar ta cutar ta COVID-19, zai iya lalata habakar tattalin arzikin nahiyar wanda daman ya ki gaba, ya ki baya.
Babbar sakatariyar hukumar, bera Songwe, ta yi nuni da cewa, a bisa yanda cutar ta auka wa babbar abokiyar kasuwancin nahiyar ta Afrika watau kasar China, tilas ne cutar ta ta shafi tattalin arzikin nahiyar ta Afrika.
A cewarta, “Duk da cewa rahotanni kadan aka samu kan barkewar cutar a wasu kasashen nahiyar ta Afrika ya zuwa yanzun, amma dai a bisa ga dukkanin alamu cutar za ta yi barna mai yawa a kan tattalin arzikin nahiyar ta Afrika.
Songwe ta bayyana cewa: “Akwai yiwuwar nahiyar ta Afrika za ta rasa rabin kudaden shigarta da kashi 3.2 a bisa wasu dalilai masu yawa wadanda suka hada da tabarbarewar hanyoyin samun ta.
Ms Songwe ta koka da yanda alakar nahiyar ta Afrika da sauran kasashe ke shafan tattalin arzikin kasashen Turai, China da kuma kasar Amurka, wanda hakan ke haddasa matsaloli.
Ta ce nahiyar tana da bukatar karin sama da dalar Amurka bilyan 10.6 a fannin lafiya domin magance matsalar yaduwar cutar ta COVID-19, sannan kuma a daya bangaren asarar kudaden shigar da nahiyar za ta yi zai iya jefa ta a cikin matsanancin bashi.
Sauran kuma matsalolin da nahiyar za ta fuskanta a dalilin barkewar cutar ta COVID-19, sun hada da faduwan cinikin da za ta yi daga siyar da danyan man fetur da kimanin dala bilyan 101.
Hakanan asarar da nahiyar za ta yi a fannin yawon shakatawa a bisa barkewar cutar wanda zai sabbaba koma-baya a kan abin da nahiyar ke samu da kuma batun zuba jari wanda hakan zai kara sabbaba samar da rashin aikin yi, in ji hukumar ta ECA.
Domin samar da kariya ta musamman hukumar ta bukaci gwamnatoci da su bayar da tallafi na musaman ga masu shigowa da abinci domin su hanzarta shigowa da abinci domin tabbatar da samuwar mahimman kayayyakin abincin.

Exit mobile version