Mukhtar Anwar" />

COVID-19: Ruwan Dare Game Duniya (III)

A baya kadan, mun yi kokarin gabatar da kwayar cuta ta farko da ake kira da SARS–COB–1, wadda ta bayyana a Shekarar 2002/2003, a gundumar Guangdong na Kasar Sin (China), kafin sabuwa ta yanzu da ta bayyana a garuruwan Wuhan da Hubei, a dai can Kasar ta China. Ba ya ga wadannan Tagwayen Kwayoyin Cutuka biyu (2), akwai ma wasu, wadanda tarihin ilmin likitanci na Karnin da ya gabata, zuwa na yanzu da muke ciki, suka tabbatar da samuwarsu.

Kwayar Cutar Marburg “Marburg Birus”

Cikin Shekarar 1967 ne masana ilmin kimiyya suka tabbatar da bayyanar wannan kwayar cuta ta Marburg. A dakin gwaje-gwaje da ake kira da “Laboratory” a turance, dake a Kasar Germany ne, aka fara shaidawa da barkewar kwayar cutar. An gano wannan kwayar cutar ne a jikin wasu Birrai, ko a ce Birirrika, wadanda aka shigo da su Kasar ta Jamus, daga Kasar Uganda.

A lokacin da waccan kwayar cuta ta Marburg ta fara bayyana, sai ya zamana cewa, cikin kashi dari (100%) na wadanda cutar ke dakuma, kashi 25% ne ke cewa ga-garinku, ma’ana, ke mutuwa. Amma da tafiya ta kara nikatawa, sai ya kasance cikin Shekarun 1998 da 2000, da kwayar cutar da bayyana a Kasar Congo, da kuma cikin Shekarar 2005, zamanin da kwayar cutar ta sake bayyana a Kasar Angola, sai ya kasance, cikin kashi 100% na wadanda cutar ke farmaka, sama da kashi 80% ne ke macewa, kamar yadda rahoton Hukumar Lafiya ta Duniya, WHO, ya tabbatar.

Kwayar Cutar Ebola “Ebola Birus”

A jikin mutane ne aka fara shaida bayyanar Kwayar Cutar Ibola, sabanin yadda wasu kwayoyin cutar ake fara ganin bullarsu a jikin Tsuntsaye ko Danbobin dake tafiya a kas a gidajen mutane, irin su Kare da Kyanwa, da kuma wasu Dabbobin dake rayuwa a dokar daji, irin su Goggon Biri da makamantansu.

Cikin Shekarar 1976 ne aka shaida bullar kwayar cutar Ibola, a Kasashen Sudan, da kuma Jamhuriyar Dimukradiyya ta Congo (Democratic Republic of Congo).

A na kamuwa ne da waccan kwayar cuta ta Ebola, ta hanyar haduwar jini, ko ruwan jiki, ko tsokar jikin wanda ke dauke da cutar, mutum ne ko dabba.

 

Kwayar Cutar Rabbies “Rabies Birus”

 

Mummunar kwayar cutar Rabbies, ta kasance na tarwatsa yanayin kwakwalwar wanda ta shafa ne.

 

Masana irin su Muhlberger, sun yi jawabai iri daban-daban game da illolin wannan makirar kwayar cuta ta Rabbies, domin sun tabbatar da cewa, akwai yiwuwar mutuwa, dari-bisa-dari, ga duk wanda ya kamu da kwayar cutar, kuma bai samu cewa Likitoci sun duba shi ba.

Kwayar Cutar Smallpod (Smallpod Birus)

 

Masana sun labarta cewa, Dan’adam ya yi Shekaru dubbai a bayan kasa, yana fama da kwayar cutar smallpod. Duk cikin mutum uku (3) da suka kamu da wannan kwayar cuta, mutum guda (1) ne ke mutuwa. Biyun da suka rayu cikin wadancan ukun, suna kare rayuwarsu ne da tabbai (tabo) balo-balo a jikunansu. Da yawan lokuta ma, cikin wadanda ke rayuwar, kan hadu da cutar makanta ne!.

 

Masana tarihi sun ce, a sakamakon wannan kwayar cuta ta smallpod, kashi casa’in (90%) na “yan asalin Kasar Amurka sun mace ne a wancan lokaci. Sannan, ya tabbata cewa, Turawa masu zuwa yawon-bude-idanu ne suka shigarwa da Amurkawa kwayar cutar a wancan lokaci.

 

Masana sun tabbatar da cewa, cikin Karni na Ashirin (20th Century) kadai, mutane miliyan dari uku (300m) ne suka sheka-lahira, sakamakon wannan kwayar cuta ta smallpod a duk fadin Duniya.

 

Cikin Shekarar 1980 ce, Majalisar Lafiya ta Duniya, ta tabbatar da cewa, yanzu haka, babu sauran kwayar cutar smallpod a Duniya.

 

Kwayar Cutar Hantabirus (Hantabirus)

 

Kafin a kutsa cikin bayani, mai karatu ya sani cewa, Kwayar Cutar Hantabirus, ba sabuwar kwayar cuta ba ce, sannan, ba daga Kasar China ba ne ta samo asali ba. Tamkar dai yadda aka gabatar a baya cewa, kwayar cutar SARS–COB–2 dake haifar da cutar Coronabirus, ba yanzu ne (2019/2020) ba ta fara bayyana a Duniya. Sai dai, kwayar cutar ta farko da ta biyu (SARS–COB–1–SARS–COB–2), duka sun bulla ne a Kasar Sin (China), sabanin kwayar cutar Hantabirus.

 

Ga wanda ya karanta Jarida a yau (March 24, 2020), ko yau saurari gidajen Rediyo, zai ji a na kiran kwayar cutar Hantabirus, da sabuwar kwayar cutar da ta bulla a Kasar Sin. Me yasa wasu “Yan-jaridu, ba sa fadada bincike ne, yayin gabatar da wasu manyan ababe da ka iya jefa al’umar Duniya cikin razani?

 

Haka, idan mutum ya hau yanar Gizo a yau, zai ga mutane na ta salallami, suna aikewa da sakonnin dake cewa, wata sabuwar cuta da sunan Hantabirus, ta baiyana a Kasar Sin.

 

Abinda Wasu Kafofin Yada Labarai A Najeriya Ke Cewa Game Da Kwayar Cutar Hantabirus

 

Wani mutum a gundumar Yunnan na Kasar China, bayan gwaji da Likitoci suka gabatar a kansa, an gano yana dauke da sabuwar kwayar cutar Hantabirus, a karshe dai ya mutu. Wannan mutumi, yana zaune ne a gundumar Shandong ce ta Chanar, a kan hanyarsa ne ta komawa gida daga wajen aiki, shi ne wa’adin nasa ya cika a gundumar Yunnan.

 

Ba ya ga kafofin yada labarai da na sadarwa a Najeriya da suka kawo labarin wancan mutumi da ya gamu da ajalinsa a Chanar, sakamakon kwayar cutar ta Hantabirus, ta tabbata cewa, kafar labarai dake a Kasar ta Sin, wadda ake kira da Gulobal Tayims, “Global Times” ta tabbatar da ingancin labarin.

 

Bayyanar Kwayar Cutar Hantabirus Ta Farko (1)

 

Kwayar Cutar Hantabirus, ta samo asali ne daga Kasar Amurka, sama da Shekaru hamsin da suka gabata.

 

Masana sun tabbatar da cewa, cikin sama da Amurkawa dari shida da suka kamu da kwayar cutar ta Hantabirus, kashi talatin da shida (36%) sun rasu.

 

Cikin wata takardar da masana masu bincike game da kananan halittu (microbiologists) suka gabatar a Shekarar 2010, sun yi bayani cewa, a lokacin Yakin Korea, Sojoji dubu uku (3000) ne suka kamu da waccan kwayar cuta ta Hantabirus, wanda kashi sha-biyu (12%) na wadanda suka kamu da cutar suka ce ga-garinku, wato suka mutu.

 

Exit mobile version