Abdullahi Muhammad Sheka, " />

Covid-19: Sakamakon Gwaji Ya Wanke Ganduje Da Uwargidansa

Gwamnan Jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje da Mai Dakainsa, Farfesa Hafsat Abdullahi Ganduje, sakamakon gwajinsu ya nuna ba sa dauke da cutar Cobid-19 dake addabar duninya, kamar yadda Babban Daraktan Yada Labaran Gwamnan Jihar Kano, Abba Anwar ya shaida wa Jaridar LEADERSHIP A YAU.

“Muna yi wa Allah godiya, bisa wannan sakamako wanda ya nuna ba ma dauke da wannan cuta. Haka Allah ya so, kuma su ma wadanda ke dauke da ita za mu cigaba da yi musu addu’ar samun saukin warwarewa daga cutar ba tare da la’akari da bangaranci, kabila, addini ko kuma siyasa ba,”in ji shi.

Sannan, Gwamnan ya yi addu’ar fatan cigaba da samun kariya daga wannan cuta ta Cobid-19 a Jihar Kano, kasa da ma duniya baki-daya. “Haka kuma, kamar yadda muke kara cigaba da neman tallafi, dole ne mu tabbatar da cigaba da sauraren shawarwarin kwararru ta fuskar harkokin lfiya tare da yin aiki tare.”

Gwamna Ganduje, ya bukaci al’umma da su cigaba da wanke hannu, amfani da na’urar tantancewa, tabbatar da tsaftar muhalli, kaucewa dukkanin wani cunkoson mutane, musamman a kasuwanni da sauran wuraren haduwar al’umma da sauransu.

Ya kara da cewa, “zama a cikin gidaje ne mafi cancanta tare da kare kai. Haka kuma, ya bukaci al’ummar Nijeriya da su yi kokarin kulawa da umarnin da Gwamnatin Tarayya ta bayar da sauran matakan da ya kamata a kiyaye, domin dakile yaduwar wannan cuta.”

Bayan karbar sakamakon gwajin, Gwamna Ganduje ya tabbatar da cewa Gwamnatinsa za ta cigaba da daukar matakan dakile yaduwar cutar Cobid-19, wanda aka fara da shawarwarin masana, kwararru da sauran masu ruwa da tsaki, wadanda suka bayar da muhimman shawarawari, domin samun kariya daga wannan cuta da kuma dakile yaduwarta.

“Ya zama wajibi mu tabbatar da yakar wannan cuta ta kowanne bangare, domin samun ingantacciyar al’umma. Muna kara yi wa Allah godiya da har zuwa wannan lokaci babu wani rahoton bullar wannan cuta a Jihar Kano. Muna rokon Allah Ya kare sauran jihohin da ke kasar nan da sauran kasashen duniya.”

Ganduje ya jaddada aniyarsa ta cigaba da tabbatar da ganin ana yin aiki da umarnin da Gwamnati ta bayar na rufe iyakoki tare da tabbatar da cewa, dukkanin masu karya wannan doka an kama su, an kuma gurfanar da su gaban shari’a tare da girbar abinda suka shuka.

Sannan ya kuma yi amfani da wannan dama, inda ya gode wa Kwamitin kar-ta-
kwana kan wannan cuta ta Cobid-19, wanda Mataimakin Gwamnan Jihar Kano, Dakta Nasiru Yusif Gawuna ke Shugabanta, wanda Farfesa Abdulrazak Garba
Habibu ke taimakawa da sauran Mambobin Kwamitin, bisa kokarin da suke na magance matsalar cutar tare da sauran Jami’an lafiya, a cewar Gwamnan.

“Muna kara mika sakon godiyarmu ga Kwamitin asusun tallafi, karkashin Shugabancin Farfesa Muhammad Yahuza Bello, Mataimakin Shugaban Jami’ar
Bayero da ke Kano da mai taimaka masa Alhaji Tajuddeen Dantata da kuma sauran wadanda suka aika da gudunmawarsu irin su Alhaji Aminu Dantata, Alhaji Aliko Dangote, Alhaji Abdussamad Isyaka Rabu, Mista Lee, Bankin UBA da sauran daidaikun mutane da kungoyoyi”, in ji Ganduje.

Exit mobile version