Muhammad Maitela" />

COVID-19: Yadda Jihohin Borno Da Yobe Suka Dauki Matakan Dakile Kwayar Cutar

Ababen More Rayuwa

A kokarin da su ke yi wajen dakile barkewar cutar Coronabirus, gwamnatocin jihohin Borno da Yobe, sun dauki ingantattun matakan da su ka bayyana a matsayin wadanda za su dakile yaduwar cutar.

A hannu guda, gwamnatin jihar Borno ta dauki kwararan matakan ko-ta-kwana, ta hanyar fadada cibiyar da za a rika killace wadanda su ka kamu da cutar ‘Cibid-19’ a asibitin tunawa da Birgediya Janar Abba Kyari da ke birnin Maiduguri, domin dakile yaduwar cutar.
Bugu da kari kuma, gwamnatin jihar ta bayyana cewa ta tanadi kayan aikin gwaje-gwaje, aune-aune don gano masu dauke da kwayar cutar a babban filin jiragen sama na kasa da kasa da ke Maiduguri, babban birnin jihar Borno.
Wannan bayanan sun fito ne daga kwamishina a ma’aikatar kiwon lafiya a jihar Borno, Dafta Saliyu Kwaya- Bura a sa’ilin da yake zanta wa da manema labarai dangane da ci gaba da daukar sabbin matakan, domin dakile barkewar annobar kwayar cutar.
Dafta Kwaya- Bura ya jaddada cewa baya ga tanadar wadannan kayan gwaje-gwajen kuma, gwamnatin jihar ta sake bunkasa cibiyar da za a rinka killace wadanda su ka kamu da cutar, a wannan asibitin (Asibitin tunawa da Abba Kyari), wadda a baya aka yi amfani da ita wajen kula da masu zazzabin Lassa a watanin da su ka gabata, domin shirin ko-ta-kwana kan barkewar annobar ‘Coronabirus’.
Ya ce, ”Kuma bisa ga wannan nake kara bayyana cewa, ba mu da ko mutum daya wanda ya kamu da wannan kwayar cuta ta coronabirus a nan jihar Borno. Haka kuma, duk da wannan, ma’aikatar kiwon lafiya a jihar Borno ta dauki ingantattun matakan ko-ta-kwana hadi da sauran bangarori a cikin shirin dakile matsalar, cikin gaggawa a fadin jihar Borno”.
”Haka kuma mun dauki irin wadannan matakan a garuruwan da yan gudun hijira suke. Shirin bai tsaya nan ba, mun tura kwararrun ma’aikatan kiwon lafiya tare da isassun kayan aikin, ta hanyar hadin gwiwa da hukumomi ma’aikatu daban-daban wajen ganin aikin yana tafiya cikin tsanaki.
A wani batu na daban kuma, ta dalilin bullar sabuwar kwayar cutar COVID-19, Gwamna Babagana Zulum ya kaddamar da wani kakkarfan kwamitin da zai sake nazarin kasafin kudin jihar Borno, na shekarar 2020.
Gwamnan ya sake jaddada cewa, biyo bayan wasu matsalolin tattalin arziki ke fuskanta, sun tilasta dole jihar Borno ta sake fasalin kasafin kudin 2020 tare da daukan matakai kara kudaden shiga da jihar ke samu a cikin gida.
Gwamna Zulum ya ayyana hakan jiya, a sa’ilin da yake kaddamar da kwamitin, a gidan gwamnatin jihar da ke Maiduguri, inda ya kada baki ya ce, “Ya zame mana dole mu sa takalmin taka-tsantsan dangane da wannan annobar coronabirus wadda ta jefa tattalin arzikin duniya a cikin tangal-tangal”.
“Sannan kuma da yadda farashin man fetur ya rikito kasa zuwa dalar Amurika 30 a kowace gangar danyen mai daya a cikin watanni uku”.
Yayin da mai bai wa Gwamnan shwara kan sha’anin tattalin arziki, Mustapha Bulu, wanda kuma shi zai jagoranci akalar kwamitin, ya bukaci kara harajin kudaden shigar da jihar ke samu a cikin gida, don aiwatar da kasafin kudin.
Yayin da ita kuma jihar Yobe, ta kafa kwamitin wayar da kan jama’a a karkashin mataimakin gwamna, Alhaji Idi Barde Gubana, inda kwamitin ya ayyana wasu matakai da su ka kunshi murtar kananan ma’aikata a jihar- daga mataki na 12 zuwa kasa, da cewa su zauna gida, kar su fita aiki, kana su gudanar da ayyukan su daga can.
Jim kadan da kaddamar da kwamitin, ya fitar da sanarwa mai dauke da sa hannun kwamishina a ma’aikatar yada labarai, harkokin yau da kullum da al’adu, Alhaji Abdullahi Bego, ya ce a kokarin daukar matakan dakile barkewar annobar COVID-19, Gwamnan jihar Yobe, Alhaji Mai Mala Buni, ya bayar da umurnin kafa kwamitin are da mika akalar sa ga mataimakin sa, Hon. Idi Barde Gubana.
Kwamitin ya umurci kananan ma’aikatan jihar, daga mataki na 12 zuwa kasa su dakata daga zuwa wajen aiki, kana su zauna gida tare da gudanar da ayyukan su daga gida. Wanda matakin bai hada da ma’aikatan ma’aikatan kiwon lafiya, ruwan sha da na SEMA, yan jaridu tare da na ma’aikatar kashe gobara.
Kwamitin ya bukaci jama’ar jihar su gudanar da harkokin yau da kullum ta hanyar yin nesa da nesa da juna, lizimtar tsabta da wanke hannu da ruwan sabulu a kai a kai. Kana arinka amfani da kyalle wajen don rufe baki da hanci da kiyaye tari ko atishawa cikin jama’a.
Haka kuma, ya bukaci jama’a su takaita gudanar da tarukan yau da kullum. Kana da ba da shawara ga jama’ar da ke shigowa daga wasu bangarorin da aka tabbatar da bullar cutar COVID-19 da cewa su duba girman Allah, su killace kansu daga cudanya da jama’a tsawon kwanaki 14.
Kwamitin ya yi kira ga jama’a da shugabanin wuraren ibada da tashoshin mota da sauran su, da cewa su samar da kayan wanke hannu, a duk lokacin da mutane su ka zo shiga wuraren.
A gefe guda kuma, asibitin koyarwar jami’ar jihar Yobe (YSUTH) ta dauki karin matakan dakile yaduwar kwayar cutar Coronabirus a jihar.
daukar karin matakin ya zo ne a takardar sanarwar manema labarai, mai dauke da sa hannun babbar jami’ar hulda da jama’a a asibitin koyarwar- Malama Hadiza Musa, ranar Larabar da ta gabata, a birnin Damaturu.
“Biyo bayan barkewar annobar kwayar cutar Coronabirus a wasu jihohin Nijeriya, ya jawo hukumar gudanarwar asibitin amincewa da daukar wasu sabbin matakan dakile bazuwar kwayar cutar”.
”Matakan sun kunshi dakatar da duk wani wanda zai ziyarci majinyacin da yake kwance a asibitin, har illa-masha Allahu, face mutum daya aka yarda ya kasance tare da majinyacin inda yake kwance”.
”Sannan idan wata bukata ta taso, mutum daya kawai aka lamunce ya raka majinyacin zuwa wasu bangarorin asibitin, wajen duba majinyacin, domin rage cunkoson jama’a”.
”Kuma kowane likita zai rika ziyartar majinyatan cikin kankanin lokacin da aka kayyade masa, don gudun kar a samu tsaiko da cunkoso a sassan da ake da bukata”.
”Haka zalika kuma, su ma sauran bangarorin dakunan gwaji, masu daukar hoto-har-hanji (radiologic), da kula da magunguna, za su rika gudanar da aikin bisa tsari cikin hanzari, amma bangarorin da basu zama dole ba, su ma an dakatar dasu”.
”In ban da na aikin gaggawa kadai, su kam za su ci gaba da gudanar da ayyukan su”. Da sauran matakan da za su taimaka wajen dakile yaduwar cutar coronabirus din.

Exit mobile version