Abuja, " />

COVID-19: ‘Yan Jarida Sun Yaba Wa Matakan Gwamnatin Katsina

Shugaban kungiyar kafafen yada labarai da Ke aikawa da rahotanni Daga Katsina ta ‘Correspondents’ Chapel’, AbdulHamid Sabo ya Yaba da matakan da gwamnatin jihar Katsina ta zauka wajen takaita Yaduwar cutar COVID-19 a duk fadin jihar.

 

Shugaban ‘yan jaridan ya yi wannan yabo ne a lokacin da take gabatar da wani taron manema labarai a Katsina, Inda ya yi nuni da cewa matakan sun taimaka gaya wajen hana Yaduwar cutar.

 

Kwamared Sabo ya ci gaba da bayyana cewa rife iyakokin da suka hada jihar da sauran jihohi, da kuma wadanda suka hada Jihar ya taimaka wa Al”ummar jihar.

 

Haka Kuma Shugaban manema labaran yabyi kira ga Hukumar yaki da yaduwar cututtuka ta kasa ‘National Centre for Disease Control, NCDC,’ ta kafa cibiyar gwajin cutar ta Cobid-19 a jihar.

 

Daga ya yi kira ga gwamnatin tarayya ta kafa cibiyoyin da ake kebe wadanda suka kamu da wannan cuta a jihar. Ya kuma roki gwamnatin da ta sakar wa jihar kudi don ci gaba da yakar wannan cuta.

 

Kwamared Sabo bai kammala jawabinsa ba Sai da ya yi jinjina ta musamman bisa kokarin da kwamitin yaki da wannan cuta na jihar, karkashin jagorancin Mataimakin Gwamna, Alhaji Mannir Yakubu, musamman bisa yadda suka samu samar tara Sama da Naira Militan150 don yaki da cutar.

Exit mobile version