Umar A Hunkuyi" />

Covid-19: ’Yan Nijeriya Uku Sun Mutu A Amurka

Jakadan ofishin jakadancin Nijeriya da ke New York ta kasar Amurka, Mista Benaoyagha Okoyen, ya tabbatar da mutuwar wasu ‘yan Nijeriya uku a dalilin kamuwarsu da annobar nan ta Koronabairus a can kasar ta Amurka.

Okoyen ya shelanta hakan ne a cikin wata sanarwa da ya fitar a birnin New York a ranar Asabar da yamma.

Jakadan ya ce daya daga cikin mamatan kwararren Likita ne da ya fito daga Jihar Abiya, wanda kuma ya kamu da cutar ta Korona ce a lokacin da yake bakin aiki a wata cibiyar kebance masu dauke da cutar a birnin na New York.

Sannan sai Jakadan ya bayyana mutum na biyu dan Nijeriya da ya mutu a sakamakon kamuwa da cutar da cewa wani dalibi ne wanda yake ajin karshe a Jami’a da yake karantar Injiniyarin a Jami’ar Western Michigan Unibersity, mai kuma kimanin shekaru 25 da haihuwa a Duniya wanda kafafen yada labarai na kasar nan suka bayar da labarin mutuwar na shi.

Okoyen ya ce: “Tare da jimami da takaici ina shelanta maku mutuwar ‘yan Nijeriya guda uku wadanda suka mutu a sakamakon kamuwa da cutar Korona a nan kasar Amurka.

“Mutum na farko ita ce wata mata mai kimanin shekarun haihuwa 60 mai suna, Hajia Laila Abubakar Ali, ‘yar asalin Jihar Kano, wacce ta rasu a ranar 25 ga watan Maris, a lokacin da take karban magani a Asibitin, Lincoln Hospital da ke Brond, New York.

“Mamaci na biyu kuwa shi ne, Bassey Offiong da ya fito daga Kalaba, wanda dalibi ne a ajin karshe da yake karantar Injiniyarin a Jami’ar Western Michigan Unibersity, Kalamazoo, ya rasu a ranar Asabar, 28 ga watan Maris, a Asibitin Beaumont Hospital a can Royal Oak.

“Sai abin takaici na uku, mutuwar wani kwararren Likita mai suna Dakta Caleb Anya, wanda ya fito daga Ohafia ta Jihar Abiya.

“Ya mutu ne a fagen yaki da annobar ta Korona a birnin New York, a ranar 1 ga watan Afrilu.

A madadin ofishin jakadancin Nijeriya da ke birnin New York, ina mai mika ta’aziyyarmu ga iyalan mamatan.

Jakadan ya yaba da sadaukarwar da jami’an lafiya da sauran ma’aikata masu gabatar da mahimman ayyuka na musamman da suka sadaukar da rayuwarsu domin ceto sauran al’umma.

“Yabo na musamman da jinjina ga kwararrun Likitocin Nijeriya da suke yin aiki a nan birnin New York, domin hidimta wa al’umma a irin wannan mawuyacin yanayin,” in ji Jakadan.

Exit mobile version