Biyo bayan yaduwar cutar Korona da ta addabi duniya bakidaya, sai ga shi wata matashiya ’yar asalin jihar Kogi mai yiwa kasa hidima (NYSC) a babban birnin tarayya, Abuja, Moribin Rosemary, ta bada gudunmawar alawus dinta na watan Maris ga gwamnatin jihar Kogi a matsayin tallafinta wajen yaki da cutar mai saurin hallaka jama’a, wato Cobid-19.
Tun da farko sai da ’yar kishin kasar ta bada tallafin sinadaran wanke hannu (Hand Sanitizers) guda 24 a ranar 24 ga Maris din ga kwamitin da gwamnatin jihar ta kafa, don dakile cutar a fadin jihar.
A ta bakin Rosemary ta ce, “Ina mika godiya ta ga Mai girma Gwamna Yahaya Bello a bisa kudurinsa na dakile cutar mai hadarin gaske. Na mika wannan gudunmawa na kudi da kuma sinadaran wanke hannu ne, don tallafa wa gwamnati a kokarin da ta ke yi na yaki da kuma dakile cutar Korona a jihar Kogi kuma har ila yau Ina addu’ar Allah Yasa jihar Kogi ba ta cikin jihohin da cutar ta shafa.”
Misis Rosemary ta kuma kara da cewa, “don ganin an shawo kan cutar, Ina kira ga jama’ar jihar Kogi da su bi umarnin gwamnati na nesa da juna wajen cudanya da kula da tsafta da kuma yawaita yin amfani da sinadaran wankin hannu (Hand Sanitizers).”