Muhammad Maitela" />

COVID-19: Yobe Za Ta Rufe Kan Iyakokinta

Gwamnan jihar Yobe, Hon. Mai Mala Buni, ya bayar da umurnin rufe kan iyakokin jihar tsakaninta da makwabta daga tsakiyar daren ranar Talatar 31 ga Maris, 2020, domin yin kan-da-garki da dakile fantsamar kwayar cutar kwarona bariyos (Coronavirus) zuwa cikin jihar.

Gwamnan ya sanar da hakan cikin sanarwar manema labarai, wadda ta fito daga ofishin Daraktan sa na yada labarai da hulda da gidajen jaridu, Alhaji Mamman Mohammed, ranar Lahadi a fadar gwamnatin jihar da ke Damaturu.
Ya ce, Gwamna Buni ya ayyana cewa daukar matakin ya zama dole, biyo bayan yadda kwayar cutar ke ci gaba da fantsama a fadin kasar nan.
Bugu da kari kuma, Gwamna Buni ya bayyana godiyar sa ga Allah Madaukakin Sarki, wanda bisa kiyayewar sa ga jama’ar jihar, inda har kawowa yanzu babu mai dauke da kwayar cutar a fadin jihar.
“Duk da kasancewar babu mai dauke da cutar kwarona bariyos (Coronavirus) a duk fadin jihar Yobe, gwamnati ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen daukar kwararan matakan kariya, ta hanyar samar da cibiyoyin killace wadanda suka kamu da ita hadi da kayan aiki tare da kafa kwamitin da zai sa ido kan cutar, a karkashin mataimakin Gwamna, Alhaji Idi Barde Gubana”. In ji shi.
Har wala yau kuma, ya ce, baya ga hakan kuma gwamnatin jihar ta samar da wani karamin kwamiti don sa ido kan duk wata cuta mai alaka ko kama da kwayar cutar a jihar, amma har yanzu babu ko mutum daya da aka tabbatar ya kamu da cutar.
A gefe guda kuma, Alhaji Mamman ya ce, Gwamna Buni ya bukaci jama’ar jihar da cewa su ci gaba da amfani da shawarwarin kwararrun likitoci kan cutar, kana kuma su guji cunkosuwa wuri guda kuma su lizimci wanke hannu lokaci bayan lokaci. Kuma su ci gaba da baiwa gwamnati hadin kai tare da sauran hukumomi a fannin yaki da annobar.
“muna kira ga yan kasuwa da su saukaka wa jama’a, kar su tsawwala farashin kaya, wanda hakan zai jefa jama’a cikin mawuyacin hali,” ya yi kira.
A karshe ya nemi al’ummar jihar da su cigaba da hakuri a fagen yin addu’o’in neman taimakon Allah ya kare jihar Yobe da ma Nijeriya bakidaya.

Exit mobile version