Hussaini Baba" />

COVID – 19: Zamfara Ta Soma Amsar Agajin Tallafa Wa Marasa Galihu 

Gwamnatin jihar zamfara karkashin jagorancin Gwamnk Bello Muhammad Matawallen Maradun ta fara karbar kayayyakin tallafi daga masu hannu da shuni da ke fadin jihar Zamfara.

 

Da yake gabatar da jawabinsa lokacin da ya ziyarci inda aka jibge kayan tallafin, gwamnan jihar Zamfara, Hon. Bello Muhammad ya gode ma wadanda suka ba da wannan tallafi kuma an take ya bada izinin ba da tallafin ga wadanda suka cancanta .

 

Gwamna Matawallen Maradun ya kara da cewa, cikin wadanda za a rabawa tallafin sun hada da gidan Marayu da makarantun almajirai da kuma jama’a wadanda suke cikin mawuyacin hali.

 

Ya kuma bukaci masu rabon kayan da su dauki kayayyakin zuwa sassan kananan hukumomi jihar.

 

“Gwamnan Matawallen Maradun ya ja kunnen manbobin kwamitin da ke rabon kayan tallafin, da suji tsoron Allah kuma ka da su kuskura su baiwa wadanda suke da hali, ya ce musamman wadanda suke cikin kwamitin.

 

Shugaban karbar tallafin, Kakakin Majalisar Dokokin Jihar ta Zamfara, Hon. Nasiru Muazu Magarya, ya bayyana ma Gwamna Matawallen Maradun yadda tallafin ya zo gare su, da kuma neman ba da umarnin raba su daga wajan Gwamnan.

 

Kuma ya bayyana wadanda suka ba da tallafin kamar haka: Sanata Ahmad Sani Yariman Bakura, wanda ya ba da kires na kwai guda dubu talatin da daya da Buhu dari na Hatsi. Sai kuma kwamishinan tsaro, Hon. Abubakar Justis Dauran  ya ba da buhu dari tare da kires na Kawai bubu daya.

 

Shi kuwa mai martaba Sarkin Zurmi Alhaji Atiku Abubakar, ya ba da buhu dari biyu na hatsi, shi kuma tsohon Minista Hon. Bashir Yuguda ya ba da miliyan biyar.

 

Shugaban jam’iyar PDP na jihar Zamfara ya ba da buhu dari biyu na masara da buhu dari na gero tare da zunzurutun kudi Naira miliyan uku.

Exit mobile version