Cristiano Ronaldo Ya Kamu Da Cutar Korona

Daga Abba Ibrahim Gwale

Dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Juventus, Cristiano Ronaldo, ya kamu da cutar Korona a yayin da yake tare da tawagar ‘Yan wasan kasar Portugal.

 

Tuni dai dan wasan ya killace kansa kamar yadda hukumomin lafiya suka bukata kuma ba zai fafata a wasan da kasar Portugal din zata buga da kasar Sweden ba a gobe.

 

Bayan tabbatar da cewa Ronaldo ya kamu da cutar suma ragowar ‘Yan wasan tawagar kasar an gwada lafiyarsu sai dai ba’a sake samun wani da cutar ba.

 

Yan wasan da suka kamu da cutar a ‘Yan kwanakin nan sun hada da Sadio Mane da Xherdan Shaqiri duka daga Liverpool inda a kwanakin baya ma xan wasa Paul Pogba na Manchester United ya kamu da cutar amma tuni ya warke kuma ya fara wasa.

Exit mobile version