Cristiano Ronaldo Ya Zura Kwallo Ta 700 A Tarihinsa

A wasan da kasar Portugal ta buga a daren jiya Litinin, fitaccen dan wasan kwallon kafarnan, wato Cristiano Ronaldo na kasar Portugal kuma dan wasan kungiyar Juventus ya zura kwallo ta 700 a tarihin kwallon kafarsa.

Duk da dai kasan ta Portugal ta yi rashin sa’ar nasara akan kasar Ukraine, inda Ukraine din ta ci su 2 da 1, amma Ronaldo ya zura kwallo 1 ta hanyar bugun daga kai sai mai tsaron gida.

Rahotanni sun bayyana cewa ya zuwa yanzu Ronaldo ya ci kwallaye 5 ga kungiyarsa ta farko wato Sporting CP guda 5, sannan ya zura kwallo 118 a lokacin da yake Manchester United, sannan ya zura kwallo 450 a lokacin da yake Real Madrid, da kuma kwallo 32 a kungiyarsa ta Juventus. Sai kuma ya ci wa kasarsa kwallo 95 wanda wannan ya kama kwallaye 700.

Exit mobile version