Connect with us

LABARAI

CSC Ta Karyata Korar Shugabanta

Published

on

Hadaddiyar kungiyar matasan masarautar Kontagora ta karyata korar shugaban hukumar kula da daukar ma’aikata a jihar Neja, Alhaji Shehu Galadima, kungiyar ta ce, labarin kanzon kurege ne.
Kungiyar ta bayyana hakan ne a wata takardar da raba wa manema labarai, da cewar wasu marasa kishin kasa da kin son zaman lafiya ne ke yada labarin a kafafen sadarwa na facebook da WhatsApp don kawai su kawo rarrabuwan kawunan jama’a a jihar, ta ce, tun kafa hukumar ba a taba samun shugaban da ya yi aiki kamar wannan shugaban ba, domin a lokacin sa ne aka samo ma’aikatan da bugi da ba su da adadi, wanda hakan ne ke kara tada hankalin gurbatattun mutane da ke shigar burtu su na wawuran kudin gwamnati alhalin dubban mutane da suka kammala karatu na zaune ba aikin yi kuma kullun ana yaushe aljihun gwamnati da sunan biyan albashi, wanda hakan ba daidai ba ne.
Dan haka muna jawo hankalin gwamnati da ta tabbatar ta yi wa mutane bayani da kuma daukar matakin gaggawa na hukunta duk wani da aka samu da cin kudin gwamnati ba bisa ka’ida ba.
“ Yanzu haka akwai rahoton da hukumar ta fitar akan wadannan ma’aikatan na bugi, dan ganin an hukunta su kamar yadda doka ta tsara” lamarin ma’aikatan bugi dai ya zama wani harkalla da ya rike wa gwamnati makogoro, wanda a kowani wata ana zaftare kudade da suna biyan albashi wanda ya wuce kima duk da cewar daruruwan ma’aikata ne ke yin ritaya wadanda wa’adin barin aikinsu ya yi amma maganar kudin albashin ma’aikata yana kara hauhawa duk da cewar ma’aikata na ta yin ritaya kasancewar wa’adin barin aikin su ya yi.
Ko a kwanakin baya ma kungiyar kwadago a jihar ta jawo hankalin maigirma gwamna akan wannan lamarin ma’aikatan bugi da kuma adadin kudaden da gwamnati ke fitar wa da sunan biyan ma’aikata wanda mai makon yayi kasa kullun yana kara hauhawa wanda wannan ba daidai ba ne a sanya ido yana cigaba da lakume kudaden da gwamnati za ta yiwa jama’a aiki.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: