Connect with us

LABARAI

CSDP Ta Tallafa Wa Al’ummar Jihar Zamfara Da Kayan Koyan Sana’a 

Published

on

A kokarin da gwamnatin jihar Zamfara ke yi, karkashin jagorancin gwamna Bello Matawallen Maradun , na ganin ta farfado da hukumar koyawa matasa Sana’a da ke Gusau gidan Dawa , yanzu haka , hukumar CSDP ta ba hukumar tallafin kayan koyan sana’a kala daban daban.

Maiba Gwamna Bello Matawallen Maradun shawara, a hukumar, Hajiya Amina Iliyasu Mafara ce ta bayyana haka a lokacin da take amsa tanbayoyin manaima kabarai a hedikwatar hukumar da ke Gusau .

” Hon Amina Mafara ta bayyana cewa , kokarin da gwamna Bello Matawallen Maradun yayi na gyara santoci takwas na koyan sana’a da ke cikin kananan hukumamin mu ,wadanda suka hada da , kauran Namoda ,Zurimi ,Talata Mafara , Maru da Bungudo , Gumi da Gusau yan sanya hukumar CSDP ta kawo wadannan kayan koyan sana’a dan ganin matasan mu sun dogara da kan su .

” Daga cikin kayan da hukumar CSDP ta bada sun hada da Kekunan dinki da na saka da kuma firiza da kuma kayayakin koyan sana’a daban daban dan ganin anyaki zaman kashe wando da matasa keyi a wannan jihar ta mu .

” Kuma wannan tallafin zai taimaka gaya wajen ganin matasa sun dogara da kansu kuma su taimaki iyayansu da ‘yan uwansu ,kuma garkuwa ne daga shiga bangar siyasa ko kungiyoyin da basu da ceba .

“Hon Amina Mafara tayi kira ga matasan da zasu gajiyar wannan shirin na koyan sana’a da su maida hankali su kware akanta dan taikamakon kasu da kansu .

” A karshe tayi kira da suci gaba dayi ma gwamnatin jihar Zamfara ,karkashon jagorancin gwamna Bello Matawallen Maradun addu’a dan ganin kudirnta ya cika na cigaban alummar jihar Zamfara .
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: