Connect with us

LABARAI

CSDP Ta Tallafawa Karamar Hukumar Munya

Published

on

An yi kira ga al’ummar yankin Shashayi, Sabon Dangunu da Salapai, Lubudna da ke karamar hukumar Munya da su tabbatar sun mallaki katin zabe dan sake baiwa gwamnati goyon baya, duk da irin halin da ake ciki gwamnati na bakin kokarinta na ganin ta samar da abubuwan more rayuwa ga al’ummomin karkara. Kwamishinan sayarwa ta jihar Neja, Alhaji Danjuma Sallau ne ya bayyana hakan a lokacin da yake bayani kaddamar da ayyukan hukumar samar walwala da ci gaban yankunan karkara ( CSDP) da ya gudana a Sarkin Pawa na karamar hukumar Munya.
Sallau ya ce wannan kudin da CSDP ta ware za a bada su kashi uku ne dan bunkasa wutan lantarki, ruwan sha da samar tsarin kiwon lafiya, idan wadanda abin ya shafa sun aikin yadda ya kamata za biya kashi na kudin ba tare da bata lokaci ba. Ya ci gaba da cewar wannan shirin ne na bakin duniya, inda za ta bada kashi goma yayin da gwamnatin tarayya za ta biya kashi tis’in wanda kuma za a biya bashin a cikin aljihun gwamnatin jiha.
Ruwan sha mai tsafta, ingantaccen tsarin ilimi da samar kiwon lafiya mai inganci ne muradin gwamnatin Alhaji Abubakar Sani Bello, dan ina jawo hankalin ‘yan uwana mutanen karkara da mu ci gaba da marawa gwamnatin jiha baya dan samun damar kammala ayyukan da ta sanya a gaba.
Tunda farko dai CSDP za ta kashe naira 2,611,696,50 akan aikin samar da ruwan sha a yankin Salapai, ya yin da 4,334,826,60 zai tafi gun gyaran kananan asibitoci, magunguna da kayan aiki, ya yin da 2,013,530,40 zai tafi gurin gyaran dakunan kwana na ma’aikatan asibitin. Sai Lubudna da za a kashe 4,142,540,25 zai tafi a bangaren kiwon lafiya, sai 4,460,258,25 zai tafi a bangaren ilimi, inda za a gina ajujuwa uku da ofishin ma’aikata da wajen ajiyar kaya.
Sabon Dangunu kuwa za a kashe 774,000,00 wajen gina fanfon burtsatse, sai naira 3,524,235,75 zai tafi wajen gina dakin shan magani, kayan aiki da msgunguna. Yayin da za a kashe 4,445,610.75 wajen gina ajujuwa uku, ofishin malamai da ajiyar kaya.
Hukumar ta ci gaba da cewar Shashayi za taci moriyar 7,108,195.50 wajen dan samar da wutan lantarki, yayin da za a kashe 1,557,360.00 wajen gina fanfon burtsatse a yankin.
Danjuma Sallau ya ci gaba da cewar duk wadannan ayyuka ne na raya kasa dan inganta rayuwar al’umma da gwamnatin Neja ta sanya a gaba, dan haka yana janyo hankalin jama’a da su kara baiwa gwamnatin tarayya da ta jiha goyon baya domin maigirma shugaban kasa, Muhammadu Buhari yana da kyakkyawan manufa ga al’ummar kasar nan, akan wannan kudurin na sa ne ya baiwa maigirma gwamna, Alhaji Abubakar Sani Bello kwarin guiwar mayar da hankali wajen inganta rayuwar al’ummar karkara.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: