Cunkoso A Gidan Yari: Yadda Mutum 1400 Ke Zaman Jiran Shari'a A Nasarawa
  • English
  • Business News
Thursday, October 9, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Cunkoso A Gidan Yari: Yadda Mutum 1400 Ke Zaman Jiran Shari’a A Nasarawa

byZubairu M Lawal
2 years ago
Gidan yari

Shugaban hukumar kula da gidajen yarin Jihar Nasarawa, Mista Yunusa A. Ibrahim ya shaida wa kwamishinan shari’a na jihar, Barrister Labaran Shuaibu Magaji halin da gidan yarin ke ciki na cin koson da ake fama sakamakon jan kafa wajen gudanar da shari’a.

Ya dai bayyana hakan ne a wata ziyara da kwamishin shari’ar ya kai ofishin shugaban hukumar kula da gidajen yarin da nufin hadin kai domin gudanar da aiki tare, masamman wajen ganin an kawo karshen rage aikata laifuka a fadin jihar.

  • Kotu Ta Yankewa Wasu Matasa 2 Hukuncin Zaman Gidan Yari Kan Gudun Wuce Kima A Kan Dokuna
  • Kotu Ta Tsare Wani Saurayi Wata 12 A Gidan Yari Bisa Barazana Ga Tsohuwar Budurwarsa 

Mista Yunusa ya bayyana damuwarsa kan yadda ake jan kafa wajen gudanar da shari’ar mutanin da ake zargi da aikata laifuka a Jihar Nasarawa.

Ya ce gidajen yari da ke Jihar Nasarawa ya cika da mutane sakamakon rashin yi wa wadanda ake zargi shari’a da za su san matsayinsu.

Ya ce adadin mutum 1,321 ake da matsuguninsu a gidajen yarin da ke fadin jihar, da suka hada da na Lafiya, Wamba, Keffi da kuma Nasarawa. Amma yanzu akwai mutum 2,069 da yawansu ya haifar da cin koson a gidajen yarin.

A cewarsa, cikinsu masu zaman jirar shari’a sun kai 1,408, sannan kan yanke wa mutum 640 hukuncin zama a gidan yari. Ya roki Kwamishinan shari’ar da ya sanya baki ga kotun da su rika gabatar da shari’a a kan lokaci domin zai rage cin koson jama’a a gidajen yari.

kwamishinan shari’a, Barrista Magaji ya ce kuddurin gwamnatin Injiniya Abdullahi Sule shi ne, samar da dauwamammiyar zaman lafiya da hukunta duk wani mai laifi ta hanyar shari’a.

Ya ce ma’aikatar shari’a ta daukarwa kanta nauyin ziyararta bangaren hukumomin da ke da alaka da shari’a, kuma wannan koken da kuka gabatar za a tabbatar an warwareshi nan ba da jimawa ba.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Ni Ne Ɗan Siyasa Mafi Shahara A Kudu Maso Gabas, Ba Peter Obi Ba – Orji Kalu
Siyasa

Ni Ne Ɗan Siyasa Mafi Shahara A Kudu Maso Gabas, Ba Peter Obi Ba – Orji Kalu

October 9, 2025
Tattalin Arziƙin Nijeriya Ya Ƙaru Da Kashi 3.9 – Bankin Duniya
Manyan Labarai

Tattalin Arziƙin Nijeriya Ya Ƙaru Da Kashi 3.9 – Bankin Duniya

October 9, 2025
Majalisa Ta Nemi Jami’an Tsaro Su Ceto Daliban Jami’ar Gusau 30 Da Aka Sace
Labarai

Kafa ‘Yansandan Jihohi Na Da Matuƙar Muhimmanci Wajen Magance Matsalar Rashin Tsaro

October 8, 2025
Next Post
Ma'adanai

Matakan Fara Sana’ar Hakar Ma’adanai Bisa Doka A Nijeriya

LABARAI MASU NASABA

Kofin Duniya U-20: Argentina Ta Lallasa Nijeriya Da Ci 4-0

Kofin Duniya U-20: Argentina Ta Lallasa Nijeriya Da Ci 4-0

October 9, 2025
Ni Ne Ɗan Siyasa Mafi Shahara A Kudu Maso Gabas, Ba Peter Obi Ba – Orji Kalu

Ni Ne Ɗan Siyasa Mafi Shahara A Kudu Maso Gabas, Ba Peter Obi Ba – Orji Kalu

October 9, 2025
HOTUNA: Yadda Obasanjo Ya Ƙaddamar Da Sabuwar Cibiyar Taron Ƙasa Da Ƙasa A Bauchi

HOTUNA: Yadda Obasanjo Ya Ƙaddamar Da Sabuwar Cibiyar Taron Ƙasa Da Ƙasa A Bauchi

October 9, 2025
Tattalin Arziƙin Nijeriya Ya Ƙaru Da Kashi 3.9 – Bankin Duniya

Tattalin Arziƙin Nijeriya Ya Ƙaru Da Kashi 3.9 – Bankin Duniya

October 9, 2025
Tawagar Likitocin Sin Dake Saliyo Ta Gudanar Da Tiyatar Dashen Yatsa Irinta Ta Farko

Tawagar Likitocin Sin Dake Saliyo Ta Gudanar Da Tiyatar Dashen Yatsa Irinta Ta Farko

October 8, 2025
Babban Yankin Sin Ya Soki Lamirin Kalaman Aware Na Jagoran Yankin Taiwan

Babban Yankin Sin Ya Soki Lamirin Kalaman Aware Na Jagoran Yankin Taiwan

October 8, 2025
Yawan Zirga-Zirgar Jiragen Kasa Tsakanin Sin Da Turai Kan Layin Dogo Na Tsakiya Ya Zarce 3,000 A Bana

Yawan Zirga-Zirgar Jiragen Kasa Tsakanin Sin Da Turai Kan Layin Dogo Na Tsakiya Ya Zarce 3,000 A Bana

October 8, 2025
Majalisa Ta Nemi Jami’an Tsaro Su Ceto Daliban Jami’ar Gusau 30 Da Aka Sace

Kafa ‘Yansandan Jihohi Na Da Matuƙar Muhimmanci Wajen Magance Matsalar Rashin Tsaro

October 8, 2025
Adadin Kudaden Da Gidajen Sinima Na Sin Suka Tara Yayin Hutun Bikin Ranar Kasa Ya Haura Yuan Biliyan 1.7

Adadin Kudaden Da Gidajen Sinima Na Sin Suka Tara Yayin Hutun Bikin Ranar Kasa Ya Haura Yuan Biliyan 1.7

October 8, 2025
Tinubu

Tinubu Na Son A Saka Hannun Jari Da Kuɗaɗen Fansho A Ɓangaren Mai Da Iskar Gas

October 8, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Exit mobile version