Cutar Bakon-Dauro Ta Lakume Rayukan Yara Bakwai A Kano

A cikin makon da ya gabata ne, al’ummar Unguwar Kurna da ke Karamar Hukumar Dala cikin birnin Kano, suka gamu da ibtila’in bullar wata cuta da ake da Cutar Bakon-Dauro. Wannan cuta dai, ta kan kama kama kananan yara ‘yan kasa da shekaru biyar lokaci bayan lokaci. A wani rahoto da Mane ma labarai suka samu da farar safiyar ranar Litinin din da ta gabata, ya nuna cewa kawo zuwa lokacin hada wannan rahoto, an samu labarin kamuwar yara kimanin guda bakwai wadanda suka kamu da wannan cuta, suka kuma riga mu gidan gaskiya.

Har ila yau, Jaridar Leadership A Yau, ta samu zanta wa da wasu daga cikin wadanda abin ya shafa kai tsaye, sun kuma bayyana bukatarsu ga Gwamnan Jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, da ya yi kokarin duba wannan matsala domin kawo wa al’ummar wannan yanki daukin gaggawa, sakamakon irin tashin hankalin da suke ciki a halin yanzu.

Haka zalika, a yayin da Wakiliyarmu ta tuntubi babban Sakataren Hukumar lafiya a matakin farko na Jihar Kano, Dakta Tijjani a kan wannan matsala ta bullar wannan cuta cewa ya yi, akwai Jami’i guda a Ma’aikatar lafiya ta Jihar Kano, wanda alhakin duba wannan matsala ke karkashin ikon ofishinsa. Daga nan ne, ya kuma ba da tabbacin cewa, zai gaggauta tura

Jami’ansu domin duba halin da wannan yanki ke ciki a halin yanzu, kana su dauki irn matakin gaggawar day a dace, in ji shi.

Exit mobile version