Kwararru al’amarin daya shafi kiwon lafiyar al’umma sun yi gargadin cewa wata cuta da ake kamuwa da ita ta hanyar jima’i za ta iya zama sabuwar cutar da ba ta jin magani idan mutane ba su dauki matakan kariya daga gare ta ba.
Cutar da ake kira da suna Mycoplasma Genitalium (MG) ba ta nuna wasu alamomi idan mutum ya kamu da ita, amma za ta iya sanadiyar ciwon mara, wanda zai iya sa mace ta kasa samun juna biyu, wato rashin samun daukar ciki.
Ba lalle ba ne mutum ya san ya kamu da ita cutar cutar MG ba kuma idan ba a dauki matakan da suka kamata ba, to za ta iya komawa cutar da ba ta jin magani.
Kungiyar kula da masu ciwon sanyi da kuma HIB ta kasar Birtaniya ta kaddamar da wani sabon tsari.
Shin mecece cutar MG?
Mycoplasma Genitalium wata nau’in kwayar cutar Bacteriya ce da ke sa ciwon mafitsara a maza, abin da ke sa suna jin ciwo idan suna yin fitsari tare da fitar da wani miki.
A jikin mata kuma, kwayar cutar na sa ciwon mara (a mahaifa da kuma kunnen mahaifa) da zazzabi da kuma zubar da jini a wasu lokuttan.
Ana kamuwa da cutar ne ta hanyar yin jima’i ba tare da kororon roba ba da ya kamu da cutar. Kororon roba ya na hana yaduwar cutar.
A shekarun 1980 ne aka fara gano cutar a kasar Birtaniya kuma ana kyautata zaton ta shafi kashi daya zuwa biyu na al’ummar kasar.
Cutar MG ba ta cika bayyana alamominta ba, kuma ba ko yaushe ne ake bukatar magani ba.
Kungiyar kula da ciwon sanyi da kuma HIB ta bayyana cewar wannan abin damuwa ne. An dai kirkiro da nau’rar gwajin cutar MG.
Sai kuma wani abu daban babu su a asibitoci koda yake likitoci a Birtaniya za su iya tura da samfurin gwaji zuwa dakin gwaji na gwamnati domin samun sakamako.
Za a iya ba da maganin Antibiotics – sai dai kuma wani abu ita cutar tana bijirawa wadansu magungunan.
‘An Gano Ashe Har Na Kamu Da Cutar MG’
John wanda ba shi ba ne sunan sa na gaskiya ba – ya tuntubi kafar gidan rrediyon BBC domin ya ba da labari kan yadda ya rika fama da cutar.
Ya bayyana cewar “A bara ne aka bayyana cewa ina dauke da cutar bayan na hadu dab wata sabuwar budurwata.”
“Dukkan mu mun je an yi mana gwaji kuma an ce babu wata cuta tare da mu lokacin da muka fara soyayya, sai dai asibitoci ba sa gwajin cutar MG idan alamominta ba su bayyana ba.”
“Bayan wata guda sai na fara jin wasu alamomi – matsanancin ciwo idan ina fitsari da kuma fitar wani miki a mafitsarata – sai dai ban san abin da yake faruwa ba.”
“Bayan wasu ‘yan makonni sai ta bayyana cewa na kamu da kwayar cutar, amma budurwata lafiyarta kalau take, kuma wannan bai yi ma’ana ba. Sai dai kuma da aka sake yi mata wani gwaji, inda a nan ne aka gano cewa tana dauke da kwayar cutar.”
“An ba mu maganin da muka rika sha har na tsawon makonin biyu, amma mun yi kwanaki biyar ba mu sadu da juna ba domin mu tabbatar mun warke.”
“Sai dai asibiti kula da masu ciwon sanyi sun ki su yi wa budurwata shi gwaji saboda ba ta nuna alamomin ba.”
“Ina ganin ya kamata asibitoci su rika gwajin cutar MG a matsayin daya daga cikin ciwon sanyi saboda tun farko da an gano ina dauke da cutar.”
‘Ba ta jin magani’