Idris Aliyu Daudawa" />

Cutar Da Ke Yi Wa ‘Yan Nijeriya Kamun Farad Daya

Ita wannan  allurar rigakafin akan yi ma mutum ita tun yana dan Jariri a  Asibiti, saboda samun kariya daga kamuwa da cutar . Binciken da aka yi ya nuna cewar cutar Hanta wato Hepatitis B ta zamo cutar da ke sanadiyar mutuwar mutane a boye ne. Masana bangaren kiwon lafiya sun ce cutar ta fi kisa fiye da cutar Maleriya a ko wacce shekara.

Binciken ya kara jaddada cewar kimanin mutane miliyan 257 ne ke fama da cutar samfurin ‘B’ a duniya, kuma kuma kasar Nijeriya na daga cikin kasashe biyar da ke da kashi 60 na masu fama da ita wannan cutar. Masu fama da cutar na yawan maganganu akan cewar idan mutum ba mai wadata ba ne abu ne mai wahala ya warke daga ita cutar ta Hanta.

Ibrahim Na-Yahaya wani bawan Allah ne da ya yi fama da cutar amma ya warke, ya kuma shaida wa BBc Cewar: “ Tun daga ranar da ya kamu da cutar, ya sha magunguna har ma ya warke, sai dai likitan shi, ya ce mashi idan lokacin zafi ya zo na dinga yawan shan maganinta.

“Na kusa shekara biyar ina fama da ita, amma na warke yanzu. Magungunanta nada tsada kwarai da gaske sosai, kuma a baya ma wahala suke sha kamar yadda ya bayyana.”

Yaya Cutar Ta Ke? Cuta ce da ke yi wa mutane kisan mummuke ba kuma  bata wani lokaci take yi ba. Dokta Nura Abubakar na kungiyar likitoci reshen jihar Kano a Nijeriya ya yi karin bayani kan yadda cutar ta ke. Cuta ce da kwayoyin cuta da ake kira birus ke haifar da ita. Kuma nau’i- nau’i ce akwai Hepatitis A, B C, D, E har da ma G.

Wadanda Aka Fi Sani Su Ne Biyar Na Farko: A da E ana samun su ne ta hanyar bayan gida,”idan mai cutar ya yi bayan gida, aka yi rashin sa’a aka yi amfani da ruwan kwatamin to sai wani ya dauki cutar,” in ji Dokta Nura.

Hepatitis B da C kuma su fi illa, don har ita C ta kan jawo cutar sankarar Hanta. B da C a kan same su ta hanyar jima’i ko ta karin jinni wanda ya kunshi kwayar cutar. “Ko kwanan ma na san wajen mutum biyar da a ka yi masu karin jini da jinin masu dauke da Hepatitis B, hakan ya sa su ka kamu su ma,” a cewar likitan.

Exit mobile version