Hukumar Lafiya ta Duniya, WHO ta bayyana cewa, cutar Ebola na ci gaba yaduwa cikin gaggawar da ba a taba ganin irinta ba, bayan watanni takwas da sake barkewarta a Jamhuriyar Demokradiyar Congo.
Dimbin jama’a ne suka kamu da cutar a cikn makwanni biyu da suka gabata, abin da ke haifar da koma-baya wajen yaki da ita, yayin da kuma rikicin ‘yan tawaye ya hana jami’an kiwon lafiya isa yankunan da Ibtila’in ya shafa.
WHO ta bayyana cewa, yawan wadanda suka kamu da cutar a makwanni biyu da suka shude sun kai 129, in da a makon farko aka samu mutane 57, yayin da a mako na biyu aka samu mutane 72 kamar yadda Christian Lindmeier, mai magana da yawun WHO din ta bayyana.
Lindmeier ta ce, mutane na ci gaba da kamuwa da cutar ba tare da daukar matakan kariya ba. A halin yanzu dai, cutar ta kashe mutane 676, yayin da 406 suka kamu da ita, in da kuma 331 suka yi katarin warkewa daga annobar.