Abubakar Abba" />

Cutar ‘Ebola’ Na Yi Wa Gonakin Tumatir Barazana A Katsina

An ruwaito cewa, wasu gonakai da a ke yin noman Tumatir a dake a yankin Mairuwa cikin jihar Katsina, cutar Tumatir da ake kira Tuta Absoluta ta aukuwa masu

A na kuma kiran cutar da sunan Tutaabsoluta mai sauran hallaka Tumatir wacce akafi sanin ta da cutar Tumatir ta  Ebola. Cutar dai, tafi yiwa manoman rani na Tumatir illa a jihar ta  Katsina.

A kakar noman Tumatir din ta bana, cutar ta Ebola, ta yiwa Tumatir illa sosai, a yayin da kuma ake da bukatar Tumatir din matuka a daukacin fadin Nijeriya.

Sai dai, manoman na Tumatir sun gaza daukar matakan da suka dace akan lokaci saboda basu da wata kwarewa ta kashe kwari.

A cewar manoman na Tumatir, sai manoman Tumatir da suke da kwarewa kan noman rani ne zasu iya dakile cutar ta tutaabsoluta yadda ya kamata idan akayi la’akari da yadda cutar take da saurin harbin Tumatir da kuma lalata shi.

Daya daga cikin manoman Tumatir kuma dilansa a karamar hukumar Funtuwa, Malam Mansur Usman ya ce, a bangaren sa, shekarun da suka gabata ya samu nasarar dakile cutar ta hanyar yin amfni da maganin kashe kwari mai karfi na Coragen.

Malam Mansur Usman ya ce, mun fara gano cutar ta Timatir  ta Ebola a shekarar 2015 a lokacin da manoman Tumatir da dama suka tabka asarar miliyoyin naira.

A cewar Malam Mansur Usman, amma bayan gano maganin kashe kwarin kamar irin su Ampligo, Coragen da Tihan, mun samu nasarar dakushe karfin cutar, amma a wannan shekarar bayan da wasu sababbin manoma da basu da wata isashiyar kwarewa suka zuba jarin su a fannin noman hakan ya janyo tasowar cutar.

Malam Mansur Usman ya kara da cewa, cutar tana rubanya da sauri, inda take janyowa gonakan noman Tumatir illa matuka, musamman daga watan Maris zuwa watan Yuni.

Malam Mansur Usman ya ci gaba da cewa, tana kara jimawa kan Tumatir tun daga lokacin da a ka shuka shi, inda Usman ya kara da cewa, akwai bukatar manoman sa tunda wuri su dauki matakai na dakile cutar ta tutaabsoluta tun daga matakin shuka Tumatir kamar yin gwaran gona yadda ya dace da kuma fesa magungunan na  Tihan ko na Coragen.

Shi ma wani manomin Tumatir Isah Umar Mairuwa yace, in har manomin Tumatir ya gano cewar akwai cutar tunda wuri ya kamata ya dauki matakan da su ka dace.

Manomin Tumatir Isah Umar Mairuwa ya ci gaba da cewa, bamu iya magance cutar gaba daya da wuri ba, amma a kalla zuba magungunan kwarin da su ka dace za su rage janyowa Tumatir kamuwa da cutar.

A cewar manomin Tumatir Isah Umar Mairuwa, sababbin manoman da suka shigo cikin fannin kada su gajiya wajen neman ilimi da kwarewa na noman Tumatir daga gun kwararrun manoman sa don kare Tumatir din da suka shuka daga kamuwa da cutar.

Shi ma wani manomun Tumatir kuma dilan magungunan kwari Alhaji Adamu Funtua ya ce, magungunan kwari na Coragen da kuma Tihan suna da karfin yakara cutar  ta tutaabsoluta.

Sai dai, Alhaji Adamu Funtua ya ce, maganin cutar na Coragen a yanzu ya yi karanci a kasuwa saboda ana samo shine daga kasar Kamaru, inda kuma ya yi nuni da cewa, wasu dilolin sa sun fara gurbata shi a kasar nan, inda suka yi watsi dashi suka mayar da hankali wajen yin amfani da maganin Tihan.

A cewar Alhaji Adamu Funtua, maganin na  Tihan OD 175 yana taimakawa wajen dakile  cutar ta Lepidoptera da akafi sani da tutaabsoluta.

Alhaji Adamu Funtua ya kuma koka cewar duk da gano cutar da akayiba kasar nan sama da shekaru biyar da suka gabata, har zuwa yau, daukacin matakan gwambati sun gaza wajen samar da mafita kan cutar.

Exit mobile version