Hashim Abdallah" />

Cutar Korona Da kokarinta Na Kawo karshen Bil’adama

A na sa rai da kyautata zaton cutar corona ba za ta yi tasiri a Afirika ba, amma ta fi hatsari a Afirika saboda halin ko in kula da karancin sani, musamman wajen tunkarar al’amari mai hatsari. A zahiri in aka yi duba da irin yadda duk cigaba da kayan kira da ilimin likitancin zamani da girman tattalin arziki amma duk da haka kasar Sin ta bayyana yadda cutar ta gagare ta. Har izuwa yanzu kuma ma’aikatar lafiya ta duniya ba ta ba da sanarwar samun maganinta ko rigakafinta ba.

Amma har yanzu a Afirika, watakila saboda rana ko in ce zafi ba ta cika yaduwa ko kisa ba, kodayake a kasashe masu rana kamar Saudi Arabia tana dan ta’adi da ya zarta na Afirika din ma. Watakila wannan ne ya sa wasu suke hasashen ba ta cika illata bakar fata ba. Kenan ‘melanin’ wanda shi ne sinadarin jinsi ko jini da ke sa bakar fata ya na iya kokuwa da cutar sosai. Wannan dai har yanzu hasashe ne, domin ba a gudanar da bincike a kai an tabbatar ba.
Amma abin da ya fito a zahiri shi ne, cutar ‘corona’ ba ta son zafin da ya kai digiri 70. Ko da ya ke, digiri 70 zai iya kisa ko ya dafa nama ba, amma tabbas zafin Najeriya ko da a arewa bai cika haura digiri 40 ba, ko hamsin ba ya kaiwa ko da a Sokoto ko Maiduguri. Ba mamaki a Agadas ta kasar Nijar ya kai 50 ko kusa ko ya dan haura da kadan. Muhimmin abu dai, zafi ba ya yi wa cutar da wasa ko kadan.
A nan arewacin Najeriya dai zafin ake tunkara nan gaba, kuma kamar yadda duk Bahaushe ya yarda Dan Adam ba a iya ma sa, amma zafin da aka fara daga ran 23 ga Maris 2020, kadai zai iya zame mana alkairi wajen fatattaka ko hana yaduwar cutar ko kashe ta. Domin mu a nan an yi sa’a har warkewa ake yi a tashi, kuma har lokacin da na ke wannan rubutu ba mutum daya aka samu tabbacin ta kashe a Najeriya. Kodayake, ba ya ba ta kadan. Ko shi wanda ya fara shigo da ita dan kasar Italiya an tabbatar da warkewarsa.
Bayan shi ma wasu mutum 2 sun warke duk da cewar wasu suna ganin wai dama zargi ne ko kamanceceniya ce ba ainahin cutar corona din ba ce. Ban san miye hujjarsu ba. Amma dai ban sani ba ko su na tunanin saboda sabuwa ce cutar ba mu da kayan aikin gwajinta, oho.
Sai dai babban abin yi, bai dace a kan zargi kawai mu ke karyata samuwar cutar ba, ko yada maganganun da ba su da tushe, abin yana da hatsari, musamman idan mun kasance maganganunmu za su yi tasiri a kunnen wasu, saboda kar mu dora su a al’amarin da zai iya illata su ko illata tunaninsu.
Addu’a ta na da matukar muhimmanci, domin an sha samun cututtuka da suka hallaka al’ummomin baya a tarihi. Sai ga shi an samu girgizar kasa a kasar Croatia a shekaranjiya waccan, wanda ya razana mutanen har a nan kasar suka fara tunanin ko an hadu da fushin Ubangiji, wanda in ya ga dama sai ya hallaka duniyar a yau, ko a yanzu.
In ka lura tsam, za ka ga a dole an zo ana amfani da maganar Annabi (S) ko a gurin wadanda ba su yi imani da shi ba, ko wadanda ba su yi imani da samuwar Allah ba ma kamar hukumomi irin na Sin masu mulkin Kwaminisanci. Wato an hana shiga, kuma an hana fita a duk inda annobar ta ke. In ka fita, za ka iya kai cutar kasashen da babu, in an bar ka da kanka ba za ka shiga inda cutar take ba. Annabi(S) ya yi gaskiya, Allahn da ya turo shi abin tsoro.
Asabar da ta gabata na ga bidiyon da ya dugunzuma min lissafi a BBC Hausa, na irin yadda cutar take fatattakar kasar Farisa wato Iran, domin har likitoci sun mutu, masu aikin jinya sun mutu, ga shi da farko da Shugabanni ta fara kisa, wato ‘yan majalisa. Duk da kasar tana da cigaban ilimi da kimiyya (za a iya tuna turka-turkar makamin kare-dangi da ake zargin sun tanada) da tattalin arziki, musamman daga man fetir, ta kai ta kawo saboda annobar cutar da yaduwa da fama, kayan aiki sun fara yanke musu, musamman iskar tallafawa lumfashi (odygen). Abin takaici, irin yadda Amurka ta sa musu takunkumin da ya jawo musu koma-baya wajen tunkarar cutar. Duk da sun nemi hakan ko don mutunta ran Dan Adam.
Duk da ba na wani shakku in aka ce asalin cutar daga dabbobi ne haramtattu, amma muryar wani bawan Allah da na ji tana yawo a kafar hirarraki ta WhatsApp yana cewa wai korona tana da asali ne da sunan Kur’ani da Turanci wato ‘Koran’. Mutumin ya ci gaba da cewa, wai saboda haramcin cin alade da sauran kayan haramun daga Kur’ani mai tsarki, su kuma kasar Sin da cutar ta fara bulla sun san suna cinsu, ga Alkur’ani ya haramta, a saboda haka, lokacin da cutar ta bulla asali daga dabbobin nan na haramci, sai suke ce mata ‘Koran birus’ ko Kur’ani bairos ko a ma’ana ana nufin ‘cutar Kur’ani’ wanda karshe ya zama ‘corona birus’ a Turance. Sai ga shi mutumin ya manta kasar Sin ba Turawa ba ne, suna takama da harshensu har mutum kan zama masani babba bai iya Ingilishi ba a Sin. Mutumin, duk a cikin rudani ko rashin sani, har ya kai ga cewa sai an daina kiranta da wannan suna za a samu lafawarta. Mu kiyaye yin magana da ka ba hujja, domin bincikena ya nuna min asalin sunanta daga harshen Girkanci ne, sannan ya shigo Ingilishi da ‘crown’ wato kan sarki, watakila saboda yanayin zubin halittar kwayar cutar da ake iya gani da madubin likita kadai.
Wani abin takaici da in aka yi wasa, zai sake janyo wani bala’in shi ne, irin yadda wani ko wasu suke ba da fatawar wai samun wani gashi a cikin Al’kur’ani a sakamakon karanta wasu ayoyi ko addu’o’i don jika shi a yi maganin kamuwa da wannan cuta. Hakika Kur’ani magani ne, amma me ya kawo gashi? Gashi ba magani ba ne in da akwai Kur’ani, ko kuma dai a ce ba mahadin Kur’ani ba ne wajen yin magani. Wani da ya yi bibiyar abin a dai ita wannan kafar WhatsApp din ya bayyana ana samun gashi a Kur’ani kamar yadda ake samu a kowane bugaggen littafi, kuma ya jarraba a littatafan boko da dama ya samu gashin, saboda ya gano ba wani abu ba ne gashin sai illa wani birbishi daga bugu daga wurin buga littatafai. Sa mutane su cigaba da wannan zai jawo wulakanta Al’kur’ani mai tsarki saboda yawan mutanen da za su cigaba da dadumarsa ba don karatu ba sai don neman gashin waraka.
Amma mu lura, duk da Najeriya har yanzu ba ta kai ga hakan ba, rufe iyakokin kasa a wannan yanayi zai taimaka kwararowar masu cutar kuma irin wannan mataki ya zo daidai da Musulunci.
Sannan shirin ko ta kwana yana da kyau kamar yadda wasu jahohi suka fara girkewa a manyan asibitoci.
Sannan, mu daure, kamar yadda suke fada, in kana da trabel history wato ka je wata kasar da take da cutar kar ka yi mu’amala da mutane don gudun yada ta. Kuma ka je a gwada ka, musamman in ka ji alamun rashin jin dadi. Bugu da kari, gano ta da wuri zai taimaka maka wajen shawo kanta tun tana karamarta.
Mun saba yin korafi da zafi, amma ko su Turawa sun yarda da abin da a ke cewa ‘fabour of nature’, ma’ana wata baiwa da haka aka same ta, ba yin kanmu ba ne, ko yin iliminmu ba ne, wanda Farfesa Aliyu Mazrui na kasar Tanzania ya ce akwai dimbin irin wannan huwacewar Ubangiji a Afirika, wato wadda ba gudunmawar kimiyya ba ce. Kamar zafi da aka yi dace muna da shi kuma yana maganinta, ko bakar fatarmu in ta kasance da gaske ne, ko kuma in an yi dace ba ta tasiri a jikin namu.
Kenan, duk da mawakin Hausa Dan Maraya Jos yana cewa in an yi zafi mu ce an yi zafi, in an yi sanyi ma mu ce an yi, to muke godewa yanayin da Allah ke ba mu. In ba a manta ba, kwanakin baya muka yi ta yayatawa an yi sanyin da ya zarta na Landan tamkar jaura ce ta wuce. Zafi kuwa ko jiya 22 ga Maris 2020 an wayi gari da shi wayewar Litinin din nan. Duk abin da ya faru dai mu godewa Allah domin ba mu san hikima ko abin da yake tafe da shi ba, domin wani lokacin shi ya sa ko ba a ji dadin abu ba, sai a ce Allah Ya sa hakan ne alkhairi.
Ku dubi Turawan yamman nan, duk da sun yi kunnen uwar shegu da kasar Iran, amma sun yarda da yin ganganko domin tseratar da al’umar kasar Italiya da cutar take barazanar shafe su daga doron kasa in ta cigaba a haka. Wannan fargabar ce, watakila ta saka Shugaban kasar Koriya ta Arewa ya yi umarnin kashe duk wanda ya kamu da cutar a kasarsu a irin nasa kamun ludayin.
kasar China dai da cutar ta fara bulla, duk da barnar da ta yi da bayyana karayar da suka yi a baya, ba su hakura ba, suka dukufa ka’in-da-na’in da tukake da feshi da wayar da kai, yanzu sun doshi kwanaki 4 ba a samu sabon kamuwa da cutar ba. Dama a baya sun gina asibiti a sati biyu kacal domin tunkarar cutar. Sun fara nasara kenan. Shin mu wani irin kimiyya da fasaha da manyan likitoci ko asibitoci ko motocin tukake muke da su? Wa zai ba mu abin feshin ko na tukaken ko ire-iren rantsattsun motocin fisa?
Ta fito fili dai, kowacce kasa a yanzu ta kanta ma take yi, in banda a baya-bayan nan da Turawa suka yarda su tura dimbin likitoci Italiya domin akwai yiyuwar cutar ta shafe su daga doron kasa.
Lallai matakan kariya da ake fada suna taimakawa in za ake aiki da su, a daure ake yin amfani da su, domin watakila in dai ba Allah ne ya so ya hallaka duniyar ba, matakan dole masu shudewa ne duk da takura mu da watakila za mu ji suna yi. Ake rufe hanci da baki yayin atishawa, ake amfani da abin makalawa a fuska don rufe hanci da baki, ake musabiha da dungu ko gefen gwiwoyin hannu, a takaita shiga taro, a takaita yawan taba wuraren da mutane suke tabawa kamar madannan girkakkun injinan fitar da kudi (ATM) da na tafi-da-gidanka (POS), da kuma abubuwan da mutane suke kamawa ko rikewa yayin tafiya kamar a matsalar benaye. A zahiri wadannan matakai sun wajaba a garuruwan da abubuwan suka bayyana.
Kuma lallai a sani wannan annoba ce da ake tunanin ba a taba irinta a duniya ba, kusan a daruruwan shekaru musamman yadda aka hana ko yin Sallar Juma’a a Ka’aba. Abin da tarin abin tsoro.
WHO, wato ‘World Health Organization’, ta yi gargadin lallai akwai abin tsoro in cutar ta fantsama Afirika. Watakila, sun fadi haka ne saboda makamantan abubuwan da na fada a baya, kamar camfi da sakaci da rashin isasshen ilimin kimiyya da kai wa kololuwar likitanci. Sai dabi’u da tunani. Hakika, mu yanzu a nan yana da wuya a iya bin sharrudan kariya na cutar, musamman in wani makusanci ya kamu.
Daga cikin irin dabi’un namu, a baya an yi korafin irin yadda wadanda suka biyo jirgin sama daga kasashen da suka kamu, su bayyana kansu amma da yawa sun yi kunnen-uwar-shegu. Masu ilimi kenan, watakila mazauna birni ma fa kenan wanda suka san hawa jirgi suka san Turai ko wasu sassan duniya.
A baya dai tun kafin cutar ta je ko’ina mun ga yadda kasar Indonesia a hotunan bidiyo suke feshin kariya da kashe kwayoyin cutar ga mutanensu da suka dawo daga kasar Sin tun yayin sauka daga matakalar jirgi. Indonesia dai babbar kasar Musulmai ce a duniya, domin ita ta fi kowacce kasa yawan Musulmai a duniya. Yanzu dai ba ta cikin kasashen da abin ya addaba, domin akwai ba sosai ba ko abin bai kai ga bayyana ba.
Lallai, ko da muna zargin cutar karya ce ko makirci ne, to mu kiyaye domin ba za ta dawwama ba. karkarinta wasu watanni.

Hashim Abdallah malami ne a makarantar Fasaha ta Binyaminu Usman da ke Hadejia a jahar Jigawa, Binyaminu Usman Polytechnic Hadejia, Jigawa State.

Exit mobile version