Connect with us

SHARHI

Cutar Korona: Ina Mu Ka Dosa A Nijeriya?

Published

on

A yayin da Ramadan yake karatowa, zai fi kyau mu fahimci cewa an rufe mu a gida tun kafin a rufe shedan.

Cutar Korona wacce ta bulla a kasar Sin, ta mamaye duniya a cikin kasa da kwanaki 100. Cutar ta sauya komai da kowa a duniya. An rufe wuraren Ibada, an rufe gidajen bushasha, an rufe otal otal na duniya, an dakatar da wasanni, an dakatar da tarurruka, an rufe masana’antu, an rufe kasuwanni an rufe tashoshin ababen sufuri, an rufe iyakoki, kowa ya koma gida ya zauna.
Sanadiyyar wannan cuta, ko ta ina a duniya ana binne gawawwaki, makabartu sun cika, marasa lafiya sun tasamma miliyan biyu, kasuwanci ya durkushe. Farashin man fetur ya fadi, an daina yawon bude ido, kasashe kowa ya daina maganan yaki da dan’uwansa.
Wannan zai zama karo na farko da duniya ta fuskanci barazana mafi girma tun bayan ci gaba na “globalization”. Wanna cuta ta Korona ta yi amfani da mafi girman ci gaba na duniya wanda ake kira “globalization” wajen yaduwa a cikin kankanin lokaci.
A Nijeriya, yau talata mun wayi gari da adadin wanda su ka kamu da cutar 343. Yanzu jihohi 20 sun samu rabon su a cikin 36 da mu ke da su. A wannan makon ne shugaban kasa ya yi jawabi ga ‘yan Nijeriya inda ya sanar da kara dokar hana yawo a wasu jihohin.
Nijeriya kamar yanda muka saba, wasu sun muzanta samuwar cutar nan inda har wani malami ya tunzura yara suna ihu suna cewa babu cutar. Har yanzu akwai mutane da dama da su ke gani wannan cuta fatalwa ce kawai. Wannan ya sa a Jihar Katsina aka samu matasa da suka yi kone-kone don an ce su yi sallah a gida.
Cewa babu cutar nan jahilci ne mafi girma. Kuma tunzura matasa su tayar da fitina da sunan malanta ta’addanci ne. Wanna cuta babu ruwanta da launin fatarka, ko addininka, ko asalinka, ko rawaninka. Malamai sun mutu sanadiyyar ta. Likitoci ma sun mutu. Talakawa sun mutu, masu kudi ma sun mutu.
Mutanenmu su sani, wannan cuta ta ci kasashe da su ka yi nesa da mu a wajen ilimin da kiwon lafiya da na’urorin samar da lafiya. A wadannan kasashe sai da ya kai a na samun mutum sama da dubu su na mutuwa a rana. A New York kadai an samu lokacin da adadin mamata ya haura 800. Shugaban kasar Italy sai da ya fito ya na kuka ya na cewa Allah ne kadai zai iya magance wa duniya wannan bala’i.
Wannan ya sa dukkan matakan da gwamnati ta dauka don kiyaye yaduwar cutar abun a yaba ne. Saboda da mai rai ake yin komai. Takaita zirga-zirga shi ne mafi girman hanya da mutum zai kiyaye kansa daga kamuwa da cutar kamar yanda likitoci suka tabbatar, saboda tasirin cutar shi ne saurin yaduwa.
Idan aka ce a bude kasuwanni da masallatai to ga abin da zai faru a misalce: Alhaji Mato ne ya je Legas sayan kaya, aka yi rashin sa’a sai ya gaisa da Mista Ojo wanda yake dauke da cutar Korona. Da ya dawo gida Jihar Kano ya kwana cikin iyalansa, washegari sai ya shiga kasuwa ya bi duk abokan harkansa guda 20 ya gaisa da su. Sannan ya je sallan jumma’a ya halarci daurin aure. Bayan an daura auren ya gaisa da mutane 20. Sannan ya je gun cin abinci aka yi ta hoto. Bayan sati daya sai Alhaji Mato ya fara wani irin tari da masassara. Aka kai shi aka gwada sai aka samu yana dauke da cutar Korona. Sai aka ce ina ya je a baya bayan nan sai ya ce Jihar Legaos. Da aka tambaye shi su waye da waye ya yi hulda da su bayan dawowar sa, sai ya zare ido. A iya wadanda zai iya tunawa dai sun kai mutum 40. Bayan wadanda ya yi ta musafaha da su a yayin daurin aure da kuma wadanda suka gaisa da shi a shago. Ga kuma iyalansa.
Wannan misalin ya ishi mai hankali ya san cewa takaita zirga-zirga da hana cunkoson jama’a shi ne mafi girman hanya da zamu yaki cutar Cobid-19.
To amma idan muka koma daya bangaren zamu ga cewa, kashi 90% cikin al’umman Nijeriya sun dogara ne da yau da kullumm wajen samar da abin da za su ci da iyalansu. Yanzu kuma an ce a koma gida. Yaya za su yi? A nan, hakki ne da ya rataye a wuyar gwamnati, dole ta samar da mafita ga mutane ta hanyar samar musu da abin da za su ci a gidajensu a yayin da suke kulle. Dole gwamnati ta fito da abinci a raba kuma a tabbatar ya iso hannun wadanda aka fitar domin su. Matukar gwamnati ta gagara yin hakan, to ta shirya zuwan fitina wanda ya fi Korona a Nijeriya.
Ina da yakinin cewa, wannan cuta da Allah ya jarrabi duniya da shi, babu wanda zai iya yaye mana shi in ba Allah ba. Saboda haka, babban abu shi ne a koma zuwa ga Allah, a dage da tuba da kuma addu’an Allah ya yaye mana. Amin.
Mai wannan rubutu shi ne, Mahmud Isa sabon Coordinator na kwamitin wayar da kan al’umma a kan cututtuka da tsabtace muhalli wacce ake kira Jibwis Health And Enbironmental Awareness.

Advertisement

labarai