Connect with us

LABARAI

Cutar Korona: Masu Sana’ar Kayan Gwari Sun Yi Asarar Miliyoyin Nairori A Kano

Published

on

Shugabanin kungiyoyin masu siyar da kayan gwari sun tafka asara ta miliyoyin Nairori sakamakon annobar korona da ta rutsa da kayayyakinsu a lokacin kulen zaman gida da aka da ya shiga wata uku ana yin sa a Kano dama dama wasu Jahuhin a Najeriya.
Alhaji mahammadu Umar na Alhaji Also, Katikan Simaila, shi ne shugaban hadadiyar kungiyar masu kayan gwari na Kano da ke kasuwar Yanlemo da Kano ya ce lokacin da aka kulle Garin Kano sunyi asara ta lemo mai yawa domin kuwa kasuwar ba shiga ba fita wanda hakan ya hadasa lalacewar lemo da sauran kayayyaki irinsu Abarba, Ayaba da sauranu.
Amma da Gwamnan Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje ya ji koken su ya tausaya musu su ne farkon bude kasuwa a Kano aka basu rana biyu a mako ta zama uku ta zama hudu a mako kuma muna saran ran za`a kuma kullim ba da dade wa ba ganin yadda Gwammana ya tashi tsaye wajen yaki da cobid-19 a Kano kuma ana samun Nasara mu kuma yan kasuwa zamu cigaba da bin dokokin Gwamnati da na Likitoci domin korar Korona a Kano.
Shi ma Malam Hamza musa shugaban kungiyar masu siyar da kankana, na Kano da ofishinsa da ke Naibawa yanLemo Kano, ya ce anyi a sarar kankana mai yawa ta miliyoyin Nairori sai da yankasuwa hankalinsu ya tashi so sai da su ka ga irin asarar da su kayi a wanan lokaci abun ya basu tsoro so sai.
Akan haka ne ya nemi shugaban kasa Mahammadu Bahari Da Gwamnan Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje ya kawo musu dauki don rage musu radadi da zafi na wanan asara da suka yi a cewar Alhaji Hamza Musa Shugaban masu kankana a Kano.
Haka kuma wakilin mu ya rowaito mana ce wa su ma ma su siyar da kwakwa sun tafka asara wata ta lalace wata an siya bashi har yanzu ba a dawo da kudin ba wan da ance mutum daya kawai daga cikin masu wanan sana a ya rasa miliyoyin Nairori a sakamakon kulle Gari dan yakar Korona.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: