Connect with us

LABARAI

Cutar Korona: Wajibi Ne Hukuma Ta Shirya Yaki Da Yunwa – Dakta Dan Bature Mai

Published

on

Shugaban kungiyar ‘Yan Kasuwa na Nijeriya Dakta Abdulaziz dan Bature Mai Gwanjo Ya ce Dolle Gwamnatin Tarayya Da Sauran Hukumomin kasar nan, Su Shirya yakar Yunwa Bayan yakin Korona da Ake yi A kasar nan, Domin Yunwama Babar Korona ne. Dakta Bature ya bayyana Haka ne a ofishinsa Dake Kano a lokacin yake hira da manema Labarai a ranar Asabar da ta gabata.
Har illa yau ya ce kulle gari da hukumomi gasar nan suka yi k matakai daban daban don yaki da korona ya jawo matsaloli na kasuwar da sauran harkokin yau da kullum kuma haka ya jawo kuma baya a dukan lamura da ya shafi rayuwar aluma kan wanan akwai bukatar lura da wanan matsala .
Dr Bature ya ce wata babbar matsala ita ce tabarbarewa tsaro da ke da matsala a harkar noma da yadda wasu ma suna hakura da noma da dai sauran matsalolin da ke kawo matsali da cikas. A wajen samar da abinci awannan kasa dan haka ne shugaban kungiyar yan kasuwar ya yi kira da shugaban kasa muhammadu Buhari ya yi amfani da maaikatar gona wajan samar da sababbun tsare tsare domin wadata kasannan da abinci wanda hakan zai sa ayi maganin karancin abinci a najeriya.
haka kuma ya bayyana cewa abangaransu na yan kasuwa sun ansa kiran gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari da na Gwamnan Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje da shawarwarin likitoci, da malamai da sauran masana akan matakan yaki da cobid 19 amatakan kasuwaninsu da ban da ban tahanyar daukar matakan kariya ashaguna da rumfunan kasuwanni da ban da ban tahanyar yin amfani da man wake hannu da sabulu da kuma amfani da takunkumin rife baki da hanci domin yakar korona, a Kano da kasa dama duniya baki daya,
A karshe Dakta danbature, ya yaba wa Gwamna Ganduje Kan Bude Ranaku Hudu A Mako wanda Ake bude kasuwannin Kano da yin sallar Jumaa wadda ya ba da dama al’ummar musulmi kara Adduar neman sauki da kawar da matsalolin da suka dami Al ummar duniya ta cutar korona da matsalolin mu na rashin tsaro da talauci da sauransu da su ke bukatar yawaita addua daga malaman mu da daukacin al ummarmu.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: