Connect with us

LABARAI

Cutar Korona: Zamfara Ta Fara Yi Wa dalibai Darasi Ta Intanet

Published

on

Gwamnatin jihar Zamfara ta hannun hukumar bayar da ilimin firamare (SUBEB) da ma’aikatar Ilim ta jihar sun fara tallafa wa tsarin shirin gabatar wa da daliban a jihar darussa ta hanyar kafafen sadarwa da kuma kimiyyar fasahar intanet, za kuma ayi amfani da gidan radiyo da talabijin na jihar da tashar talabijin na NTA dake Gusau wajen gabatar da shirye-shiryen. Babbar burin shirin shi ne samar wa yara jihar wani nau’i na karatu a daidai lokacin da ake zama a gida don dakile yaduwar cutar korona a jihar.

Shugaban hukumar SUBEB, Alhaji Abubakar Aliyu Maradun, ya ce, an samar da shirin ne don taimakawa yara cigaba da harkar iliminsu a yayin da suke zaman gida sakamakon dokar hana zirga-zirga da aka sanya a fadin jihar abin da kuma ya kai ga rufe makarantu a fadin jihar. Ya kuma kara da cewa, za a gabatar da shirin ne a lokutta daban-daban a gidajen watsa labaran da aka lissafa. Shugaban hukumar ya kuma bayyana cewa, tuni aka kashe fiye da Naira Miliyan 5 don ganin an cigaba da ilimantar da yara har zuwa lokacin da za a bude makarantu a jihar.

Ya kuma bayyana cewa, hukumar za ta cigaba da tallafawa shirin bayar da ilimi ta kafafen sadarwar koda kuwa an koma makarantu yadda aka saba. Ya kuma mika godiyarsa ga hukumar UNICEF a bisa tallafinta ya kuma bukaci masu hannun da shuni a fadin kasar nan su tallafa wa yara da daman samun karatu ta kafafen sadarwa don kare darajar karatu. Haka kuma hukumar UNICEF rehen jihar Sakkwato ta tallafawa shirin da Naira 18,496,350.
Advertisement

labarai