Cutar Kwalara Ta Kashe Mutane 45 A Kasar Zimbabwe

Hukumar lafiya ta duniya ta bayyana cewar cutar kwalara ta kashe mutane 45 a kasar Zimbabwe a cikin makonni uku da suka wuce, wannan al’amarin kuma kamar dai yadda ita hukumar ta ce, abin yana da daure kai saboda “multi- drug resistant”

An dai bayyana cewar  za ayi allura nan bada dadewa ba, za kuma  afar ta da mutane 450,000 wadanda za a yi ma mutane wurin da cutar tafi shafa a wani kauye na Harare.

Za dai a shigo da magunguna 500,000 zuwa kasar ranar Laraba wanda kuma shi ne zai kasance allura ta farko da kasar zata yi, saboda a shawo kan ita cutar ta kwalar.

Hukumar lafiya ta duniya da kuma da kuma ma’aikatar lafiya ta kasar sun bayyana an samu wadanda ake ganin sun kamau da cutar su 6,428, da kuma mutwar mutane 45 da kuma wasu al’amuran cutar da aka tabbatar da mutane 96.

Dukkannin dai mace macen sun faru ne a babban birnin kasar wato Harare da kuma wani lardin gabas na Makoni da kuma wani a cikin tsakiyar birnin Masbingo.

Rahoton ya nuna cewar birnin Harare yana gyara wasu wuraren da ake tara datti wadanda suka karye da kuma lalacewa, bayan da bulo da kuma bututun da suka fashe,  a sanadiyar haka kuma suka wuraren sun baci da yadda ruwa mai wari ke fitowa ya malale wuraren.

Ana kuma kai ruwa mai tsafta zuwa gidaje, yayin da kuma ‘yansanda suka hana sayar da abinci akan layuyyuka, suka kuma kama wwadanda suke sayar da abincin duk domin a kawo karshen  kara yaduwa da kuma bazuwar ita annobar ta kwalara.

Barkewar annobar kwalara ta sha faruwa akai akai a  biranen Zimbabwe, wuraren da ruwa mai tsafta da kuma kulawa da tsaftace muhalli yake da matsala.

A Harare an hana taron jama’a da kuma amfani da hannu wajen gaisawa.

Kasar Zimbabwe dai tsohon Shugaban kasa Robert Mugabe shi ne wanda ya mulke ta tun lokacin datab samu mulki a shekarar 1980, har zuwa lokacin da aka matsa ma shi sauka daga mulki, kasar ta hadu da wata babbar annobar kwalara a shekarar 2008. Alokacin mutane 4,000 ne suka mutu a kalla kuma mutane100, 000 suka kamu da cutar.

Exit mobile version