Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
Home RAHOTANNI

Cutar Kyanda Ta Bulla A Taraba

by Tayo Adelaja
September 18, 2017
in RAHOTANNI
2 min read
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram

Daga Mohammad Shafi’u,  Yola

Asusun kula da yara na Majalisar Dinkin Duniya wato UNICEF ya shirya taron fadakar da jama’a a jihar Taraba sanadiyar bullar cutar kyanda.

samndaads

An tabbatar da bullar cutar kyanda a kananan hukumomi goma sha hudu daga cikin goma sha shida da ke jihar Taraba da ya yi sanadiyyar mace-macen yara da dama ‘yan kasa da shekaru goma.

Babban jami’in asusun kula da yara na Majalisar Dinkin Duniya, MDD, a jihar Taraba, Dakta Zarto Philip ya sanar da haka a wani taron gaggawa da shugabannin kananan hukumomi, sarakunan gargajiya da jami’an kiwon lafiya mataki na farko gabannin soma aikin rigakafin cutar kyanda a jihar.

Uwar gidan gwannan Jihar Taraba Barrista Ana Darius Dickson Ishaku ta ce akwai bukatar sadaukar da kai a bangaren jami’an kiwon lafiya mataki na farko da ke aiki a yankunan karkara ba tare da la’akari da matsalar yanayi ko kudaden alawus da ake biyansu ba wajen aiwatar da aikinsu don kada su cutar da wadanda ke zaune a kan tsaunuka ko koramu inda babu hanyar mota.

Da yake bayanin kaifin matsalar bullar cutar kyanda a yankunan karkara, sakataren kungiyar shugabannin kananan hukumomi ta kasa reshen jihar Taraba Honorabul Idi Mali ya fadawa cewa ana samun karuwar mutuwar yara a cibiyoyin kiwon lafiya mataki na farko a ‘yan kwanakin nan sakamakon bullar cutar.

Kan gudummawar da ya dace sarakunan gargajiya su bayar wajen yaki da cutar, Galadiman Muri Alhaji Lamido Abba ya ce zasu yi Yekuwa sako-sako da lugu-lungu har sai sun tabbatar talakawansu sun rungumi shirin allurar rigakafin cutar.

Alkalumma da asusun kula da yara na Majalisar Dinkin Duniya, MDD, sun nuna an samu karuwar kamuwa da mace-macen Yara ‘yan kasa da shekara goma daga miliyan dari da casa’in a 2014 zuwa miliyan dari biyar da ashirin da bakwai a 2016 wanda a bana ake kiyasar na iya dara hakan.

SendShareTweetShare
Previous Post

An Damfari Wata Bakatsiniya A Saudiyya

Next Post

An Kafa Kwamitin Da Zai Sa Ido Kan Hakar Ma’adanai

RelatedPosts

DATA

Har Yanzu Ana Sayar Da (DATA) Kan Tsohon Farashi Duk Da Ragin Kashi 50

by Sulaiman Ibrahim
16 hours ago
0

Yawancin masu amfani da layin sadarwa sun ce har yanzu...

Farfesa Dadari

Yawan Karbo Bashin Da Gwamnati Ke Yi Bai Da Amfani Ga Kasar Nan -Farfesa Dadari

by Sulaiman Ibrahim
16 hours ago
0

Wani Malami a Jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria, Farfesa...

Gobara Ta Yi Sanadiyyar  Mutuwar Uwa Da ‘Ya’yanta Biyu A Kirfi

Gobara Ta Yi Sanadiyyar  Mutuwar Uwa Da ‘Ya’yanta Biyu A Kirfi

by Sulaiman Ibrahim
16 hours ago
0

Ibtila’in gobara ya ci rayuwar mutum uku daga ciki har...

Next Post

An Kafa Kwamitin Da Zai Sa Ido Kan Hakar Ma’adanai

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Domin sanya talla ko karin bayani a tuntube wannan numbar +2348126152609.

Leadership Epaper
ADVERTISEMENT
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us

© 2020 Leadership Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2020 Leadership Group .

Go to mobile version