Daga Idris Aliyu Daudawa
Su kwayoyin cutar sida (da Turanci HIV, da Faransanci VIH) wacce take nufin cuta mai karya garkuwar jiki, sannan kuma ana kiranta ita cutar da sunan kanjamau ko Sida a Hausance. kanjamau wata cuta ce ko ciwo ne wanda ake daukar shi ko ita, ta sanadiyar mutuwar kwayoyin halitta da suka kasance garkuwar jikin mutum daga kamuwa da wasu cututtuka. Al’amarin daya shafi kamuwa da cutar na farko, shi ne mutum ba zai iya gano alamomin ba, amma zai iya mura ta dan wani lokaci.
Cutar kuma ba zata iya daukar lokaci mai tsawo ba tare da ta nuna wata alama ba. Da cutar ta ci gaba da kafuwa, tana shafar kwayoyin halitta ne wadanda suke garkuwa ne, daga kamuwa da cututtuka a jikin mutum, sai hadarin kamuwa da wasu kananan cututtuka kamar su tibi, da cututtukan daji wadanda ke da wuyar shafar masu kwayoyin garkuwa da cututtuka masu aiki a jikinsu. Wadannan dadaddun alamomi su ake ce da su kanjamau (AIDS). A wannan lokaci yawanci wadanda suka kamu da cutar suna kai ga ramewa.
kwayoyin cutar sida na yaduwa ne ta wadannan hanyoyin; jima’í maras tsaro, da bayar da jinin mutumin daya kamu da cutar, yin amfani da allura wadda take dauke da cutar, da kuma sha daga Nonon uwa zuwa ga jariri yayin da take da juna biyu ko ta haihuwa ko ta nono (shayarwa). Ruwan jiki kamar su miyau da hawaye ba a iya kamuwa da wannan cutar HIV ta wurinsu ba. Hanyoyin rigakafi sun hada da: jimaí mai tsaro wanda aka sa kwaroron roba, shirya musayar allura, da masu dauke da cutar, sai kuma kaciyar maza. Ana iya magance ciwo daga yara ta hanyar ba su magani mai karfafa kwayoyin garkuwar jiki daga kamuwa da cututtuka, tare da iyayensu. Cutar ba ta da magani ko rigakafi, amma akwai magani mai karfafa kwayoyin garkuwar jiki daga cututtuka,wanda ke taimakawa wajen rage karfin ciwon a jiki, kuma yana kusan warkar da ciwon. Bincike ta nuna mutum zai yi rayuwa ta shekaru goma sha daya (11), sai ya mutu idan ba a yi jinyart shi ba.
A shekara ta 2015, kusan mutane miliyan 36.7 an same su da wannan kwayoyin cutar sida wanda ya kai mutuwar mutum miliyan 1.1. yawancin masu dauke da cutar ‘yan saharancin Afirka ne. Tsakanin ganowarta a shekara ta 2014, cutar kanjamau ta kashe mutum miliyan 39 a duniya duka bisa ga jimila. Kwayoyin cutar sida da kanjamau muguwar cuta ce wadda bazuwarta kamar ruwan dare ne, mai gama duniya baki daya. An fara samu kwayoyin cutar sida a yamancin tsakiyar Afirka a karshen karni na sha tara zuwa ashirin, cibiyoyin kula da hana yaduwar cututtuka (CDC) na Tarayyar Amurka ne suka fara gano ciwon kanjamau a shekarar 1981 da kuma hanyoyin kamuwa da cutar a farkon shekaru da aka gano cutar.
kwayoyin cutar sida da kanjamau ta yi matukar shafar al’umma a matsayin ciwo da kuma samun dalilin nuna wariya ga masu dauke da wannan kwayar cutar. Wannan ciwon yana matukar shafar tattalin arziki. Akwai rashin fahimta da dama game da kwayoyin cutar sida da kanjamau, kamar na cewa ana iya kamuwa da ciwon ko ba ayi jimaí ba. Ciwon ya zama abin jayayya tare da addini tare da darikar Katolika na ra’áyin rashin goyon baya amfani da roba, wajen jima’í don tsaron wani ya kamu da cutar . Wannan ya jawo hankalin kungiyar magani ta duniya da siyasa da kuma gudumawar kudi masu yawa tun da aka gano cutar a shekara ta 1980.
Muhimmancin Girar kasa Da Ta Saman Ido Ga Lafiyar Mutum
A wani bincike da masana kimiyya da fasaha suka ya nuna cewar, da akwai wasu abubuwa da suke maida fuska ta kasance abin ban sha’awa. Da yawa daga cikin mutane, su kan dauki Ido, Hanci, da kuma Baki a matsayin abubuwan da suke nuna kyan mutum a fuska. Amma sun iya gano cewa dukkan su basu kai ga gashin gira ba, na sama da kuma kasan ido ba.
Domin kuwa ita girar fuska ce ake iya ganin kyau, haka ana amfani da gira wajen bayyanar da wasu manufofi da mutun yake nufi, na daga su ko muttsuke su, da zai bayyana ma wani cewar wannan abin ba a yarda da shi ba, ko kuwa ya zama abin da aka amince da shi. Yanzu haka ‘yan-mata masu yawa su kan kashe makudan kudade don ayi musu gira ta kirkira.
Haka suma gasun sama da kuma kasan ido, su kan taimaka matuka wajen kare ido daga wasu miyagu kanana da manyan abubuwa da kan kaima ido farmaki na bazata, wadanda daga karshe na iya samar da wata cutada zata shafi lafiyar shi idon. A wani bincike da aka gudanar a jami’ar Lethbridge ta kasar Canada, an nuna ma mutane hoton wasu fitattun mutane 25 da aka cire musu gira, aka kuma nuna masu na wasu fitattu 25 da aka cire musu ido.
Kashi 56 sun iya gane wadannan mutane marasa ido, amma kashi 46 ba su iya gane su mutanen marasa gira ba, hakan dai yana nuna cewar gira na da matukar tasiri ga hallitar dan’Adam.
Aduwa Da Muhimmancinta Ga Rayuwar dan Adam
Cututtuka 8 da Aduwa take maganinsu- Jerin cutuka guda takwas da itacen aduwa yake magani a jikin dan adam – Ana amfani da ganyen, ko bawon, ko kuma dan wurin yin magunguna kala kala Tun da can mutane sun dauki aduwa a matsayin sahihin magani, sai dai kuma kowacce kasa da yadda take amfani da ita da kuma yadda take sarrafa ta wurin magani, sannan kowacce kasa da irin maganin da take yi da ita. A kasar mu ta Hausa, masu magungunan gargajiya sun cinye lokaci mai tsawon gaske suna amfani da ganye da ‘ya’yan aduwa wurin maganin wasu cutuka. Cutuka guda 8 da aduwa take maganinsu.
Ga wasu daga cikin cututtukan da Aduwa take warkar dasu
Amfanin ganyen Aduwa:
1. Ana amfani da garin ganyen Aduwa da Ricinus Communis, a tafasa da ruwan zafi a rika wanka dashi don magance kurajen fata, kazuwa, kunar wuta da kuma kaikayin jiki.
2. Ana amfani da ganyen Aduwa wurin magance cutar fitsarin jini.
3. Ana dafa bawon itacen Aduwa a rika shan ruwan domin maganin cutar kuturta.
4. Ana amfani da garin kwallon aduwa cokali daya a cikin kunun gero a rika sha akan lokaci, yana maganin tsutsar ciki
5. Ana shan ruwan ganyen Aduwa idan an dafa don maganin ciwon gudawa.
6. Ana amfani da garin kwallon Aduwa wurin maganin cutar asma, idan aka daka kwallon a tafasa asha da karamin cokali uku.
7. Ana yin kunun Aduwa ana sha ga mai yawan amai da tashin zuciya. Sannan ana amfani da kunun wurin maganin hawan jini, idan ana sha.
8. Mace wadda take shayarwa zata iya amfani da garin ganyen Aduwa a cikin kunun gero, domin tsaftace jininta da cikinta, sannan za ta samu isashen Nono ga jaririnta.