Muhammad Ibraheem Zakzaky" />

Cutar Osteoarthritis: Labari Mai Sosa Rai Dangane Da Mahaifiyata

A cikin watan Janairun 2018 da dare, ina tsammanin daren 5 ga wata ne, labari mafi sosa rai ya riske ni; cewa Mahaifina yana fama da matsanancin ciwo, ta yadda hatta magana baya iya yi, tare da sandarewar daya daga cikin hannayensa; wanda dukkansu alami ne na cutar shanyewar barin jiki. Irin wannan ciwon ba bako bane a wurina, domin Kaka ta da ta rasu, ta yi fama da makamancinsa. Tun kafin zuwan wannan lokaci, da ni da sauran ‘yan uwana muna cikin matsananciyar damuwar rashin tabbas dangane da lafiyar Mahaifina da Mahaifiya ta. Tun da jimawa, kasantuwar Mahaifina ya rasa daya daga cikin idanunsa, sai ya kasance ragowan ido dayan ma baya iya yin karatu da shi, tun bayan wani aiki da likitoci suka yi masa a farkon shekarar 2016; lamarin dake hana ni samun bacci, saboda na san ba a nuna kulawa a kai ba.

Kafin wancan aikin da aka yi masa, yana dan iya yin karatu da ragowan idon, domin kuwa tun bayan abubuwan da suka faru, an bashi gilashin ido mai karfin +9, wanda taimako daya zai iya yi mishi, shi ne ya iya karanta rubutun da suke da manyan haruffa. Duk wani kokari da muka yi don ganin an yiwa tufkar hanci, abin ya ci tura. Hatta ma yunkurin ji daga bakin likitocin da suke duba Mahaifina, abin ya faskara. Haka nan ma duk kokarin da muka yi don ganin rahoton da likitocin suka bayar na sakamakon bincikensu shi ma ya faskara. Abin da ya zo mana daga bayanan da muka samu shi ne cewa, DSS suna bibiyar likitan.

Ita kuwa Mahaifiyata, shekaru biyu kafin afkuwar lamarin da ya faru a Zariya a Disambar 2015, tana fama da cutar osteoarthritis. Duk da kasantuwar ni ba Likita bane, zan so na yi bayanin yadda cutar ta osteoarthritis ta ke, musamman ga wadanda ba su taba sanin ciwon ba.

Bincike ya tabbatar da cewa jikin mutum na da kasusuwa 260. Wadannan kasusuwan sun dogara ga wani bargo wanda ke rike da mutum. Akwai bargo da yawa wadanda suke bayar da kariya ga jikin mutum. Daga cikin irin wadannan bargon, akwai wani wanda ake kira da ‘Cartilage’, aikinsa shi ne ya taimakawa kasusuwan dake hade da juna a mahadarsu ta yadda za su iya gudanar da aikinsu yadda ya kamata. Akwai wannan bargon na ‘Cartilage’ a duk wani mahadar kashi dake jikin mutum.

Sakamakon shekaru (tsufa) ko wahala, da sauransu, wannan bargon na ‘Cartilage’ ya kan fara fuskantar barazana. Ta yadda mutum zai fara jin matsanancin zafi a duk wata mahada ta kasusuwansa, lokaci bayan lokaci. Sannan kuma yana janyo kwarewar fatar da ke mahadar kasusuwan, da gaza yin amfani da wasu bangarorin jiki, da sauransu. A takaicen takaitawa, wannan shi ne yanayin cutar Osteoarthritis.

Bayan an yi gwaji an gano cewa Mahaifiyata na da wannan matsala ta Osteoarthritis, na bibiyi likitoci mabambanta, wadanda kuma suka tabbatar min da cewa, ana tafiyar da wannan mugunyar cuta ne ta hanyar bin matakai. Da farko ana daukar matakin bin wasu tsararrun hanyoyi domin kashe kaifin cutar. Sai kuma a dora mutum akan wasu magunguna, domin a takaitawa mai ciwon (kamar Mahaifiyata) zafi da azaba, lokaci bayan lokaci har a fara ba mutum magungunan kashe radadi. Daga bisani, wadancan matakai biyu suna kai wa ga makura ta yadda mai fama da ciwon sai dai a yi tiyata don yi masa dashe. Ita wannan cutar ta osteoarthritis a haka ake tafiyar da ita, idan kuma aka kuskure wurin tsallake matakan, toh gabobin da ke fama da ciwon za su daina aiki. Kuma haka nan masu fama da ciwon za su ci gaba da rayuwa cikin matsanancin zafi har sai ranar da aka yi musu tiyatar dashen.

Dalilin da ya sa likitoci suke bin wadancan matakan a tashin farko, shi ne don su takaita batun yi wa mai ciwon dashe, har zuwa lokacin da abin zai yi kamari. Ana gujewa yin dashen ne ba don wai za a iya kaurace faruwarsa bane har abada, sai don a kaucewa hatsarin dake tattare da hakan.

A lamarin mahaifiyata, tana fama ne da cutar osteoarthritis wacce ke kama mahadar gwiwa. Tun shekaru biyu baya ta ke rayuwa cikin matsanancin ciwo mai radadi. Wannan ya sa yanzun ba ta iya yin tafiya mai tsawo, ko tsayuwa na lokaci mai tsawo. Duk wani yunkuri da muka yi don ganin DSS sun bari Kwararren Likitan Kashi ‘Rheumatologist’ ya duba ta, amma abin ya ci tura.

Sai bayan da mahaifina ya kamu da cutar shanyewar bangaren jiki ne na iya fahimta daga mahangar likitocin da suke aikin daidaita lafiyarsa, su ne suka ce; abubuwan da suka janyo mishi wannan cuta suna da yawa, daga ciki akwai batun yawan damuwa da rashin motsa jiki ga mutum mai shekaru irin na Mahaifin nawa. Sannan kuma Mahaifina na fama da cutar hawan jini, saboda jinin na yawan sauka ya hau, wani lamari wanda Kaka ta da ta rasu ta yi fama da irinsa.

Bayan da aka kyale likitocin mahaifina suka duba shi, sun kokarta ne wurin ceto shi daga shanyewar barin jikin da muna iya cewa da gangan aka haifar mishi da shi. Mutumin da ya doshi shekaru 70, yana bukatar yawaita zirga-zirga fiye da komi. Sannan kuma akwai bukatar a kiyaye duk wani lamari da zai kai ga tashin hawan jininsa. Da kuma duk wani yanayi da zai iya hana mishi yin karatu, domin shi mutum ne da ya ta’allaka rayuwarsa ga karatu. Yanzun ka sawwala cewa, ka tsinci kanka a wani yanayi wanda Matarka tana cikin matsanancin ciwo mai radadi, kai kuma ba ka da halin taimakonta, ai cutar shanyewar jiki a wurinka ma ta zo da sauki. Domin kuwa ba abu bane mai saukin dauka.

Tun bayan fama da shanyewar barin jikin da Mahaifina ya samu, ci gaba daya kawai aka samu. Shi ne cewa, Mahaifana suna samun likitoci na duba su, ma’ana likitocin da suka damu da yi musu maganin cututttukan da suke fama da su. Yanzun babu tantama na san hakikanin halin da iyayena suke ciki. A karon farko ina iya sanar da mutane gaskiyar abin dake faruwa dangane da lafiyar Iyayena; Ina da masaniya ta koli dangane da ciwon Mahaifina da na Mahaifiya ta. Na so a ce wannan abin da na sani ya zama labari ne mai dadin ji, domin al’ada ce ta bahaushe, ya rika cewa ‘Lafiya Lau’ a dukkan lamurra. Ni ma na so a ce idan wani zai tambaye ni dangane da Iyayena, zan ce lafiyansu lau. Sai dai fa, bayanan da nake da su, ba masu dadin ji ba ne. Don Allah, duk wanda ya hadu da ni, kar ya tambaye ni dangane da halin da Iyayena suke ciki, domin duk wata amsa, za ta zo a gaba cikin rubutun nan.

Duk da yake an kyale wani likita ya duba lafiyar Mahaifiyata. Sai dai kash! Ra’ayinmu daya da wannan likitan. Sau da yawa na kan kasa bacci na tsawon kwanaki, ina begen Allah ya bani tsawon rai, domin na san wadanda ke tsare da Mahaifiyata babu ruwansu da lafiyarta, son samu ne ma ta mutu a tsare. Wannan Mahaifiya ce, wacce ta yi laulayina na wata tara, tare da na sauran ‘yan uwana takwas, ita ce a yau gwiwowinta suke fama da matsanancin ciwo. Nine na farko da ya fara takurawa wadannan gwiwowi, kafin wasu mutum takwas su biyo bayana. A gaban idonta aka kashe shida daga cikin ‘ya’yanta. Ina da tabbacin cewa da yawan ‘ya’ya da iyaye sun fahimci inda na dosa, kawai ni bambancin labarina da na saura, shi ne, ni a shirye nake na kai Mahaifiyata kowanne irin asibiti ne, amma DSS sun yi min Katanga da aikata hakan.

Wannan babu batun kara gishiri a miya. Ni shaidan gani da ido ne. Domin Mahaifiyar wani abokina wacce take dauke da wannan cutar ta osteoarthritis, sai aka yin jinkirin fitar da ita zuwa kasar da za a yi mata aiki, duk da likita ya bayar da shawarar a gaggauta kai ta zuwa asibiti don a yi mata dashe. Daga karshe dai dole aka tunzura abokina wurin daukar matakin da ya dace. Domin irin halin da ya stinci mahaifiyarsa a ciki, ta rika kuka da mitar ciwo. Haka ta yi ta fama na kwanaki, ba ta iya mikewa tsaye. Cikin ikon Allah ya yi dacen kai ta asibiti a kasar Dubai. Har yau din nan ba mu son tunawa da wannan lamari mai tada hankali.

Tun a wancan lokacin, ina cikin fargabar cewa Mahaifiyata fa na iya fuskantar makamancin wannan matsala. Sai dai ni a nawa misalign, Mahaifiyata ba ta tsinci kanta a halin da take ciki bane, saboda sakacinmu. Kuma ina mai tabbatar da cewa Mahaifiyata na matukar bukatar tiyata cikin gaggawa, wanda a shirye nake na kai ta inda za a yi mata aikin. Sai dai hakan ba zai yiwu cikin sauki ba, domin Mahaifiyata tana tsare ne, a hannun wadanda ke yi mata barazana da bindiga. A wannan bigiren bani da wani abu da zan iya yi, domin ni dai ba bindiga nake da ita ba. Kuma ga shi likita ya sanar da cewa, tun tuni ya kamata a yi wa Mahaifiyata tiyata.

Bani da wata hanya da zai yiwu na san cewa Mahaifiyata na bukatar a yi mata wannan tiyatar, don wannan ne karon farko da aka bar likita ya gudanar da aiki yadda ya dace don lura da ciwon. Kuma shi ne karon farko da ni, Da ga Mahaifiyata na saurari bayanin likitan dangane da ciwon dake damun Iyayena. Likitan ya kara da cewa, Babban dalilin da ya sa Mahaifiyata ke yawan fama da ciwon ciki, shi ne don akwai birbishin alburusai har yanzun a cikin cikinta, tun Disambar 2015. Hatta muryan Mahaifiyata ya canza daga yadda yake, da ji ka san tana fama da matsanancin ciwo.

Duk da haka, ina mai godiya ga Allah da ya bani aminai dake debe min kewa ta hanyar yin muzaharori a Babban Birnin Tarayya, Abuja. Duk da zai yiwu mu kasance ‘yan kalilan a yanzu, amma zuwa nan gaba za mu kara yawa. Za mu ci gaba da yin muzaharorinmu na kin zalunci cikin lumana. Sannan kuma ina rokon Allah ya bani ikon da zan iya raba Mahaifiyata da wannan radadin ciwon da take ciki. Ba dole bane na kai ga nasara, na kuma san Mahaifiyata za ta ci gaba da shan wahala da radadin cutar osteoarthritis, kamar yadda yake a dabi’ar cutar. Ci gaba da tsare Mahaifiyata ya sa ba ni da wani iko da zan iya taimaka ma ta, duk kuwa da kasantuwar cewa zan iya daukar duk wata dawainiyar hakan.

Ina rokon Allah da ya kawo karshen zaluncin Sojojin Nijeriya, da DSS, da kuma karshen mulkin Kama-Karyan Buhari, Shugaban Kasar da ke hana a yiwa mara lafiya tiyata, musamman ma idan ka yi rashin sa’a ya kasance cewa mahaifiyarka ta tsole wa wasu daga ‘yan gaban goshin Shugaban Kasa ido.

Mohammed Ibraheem Zakzaky,

ya rubuto Daga Zariya, Jihar Kaduna

Imel: Mz4real1@gmail.com

Exit mobile version