A wannan mako cigaba ne da kawo maku hirar da muka yi da Dokta Isa Abu Abdurrahaman dangane da cutar Sikari wato diabetes, yadda abin ya kasance a makonnin da suka gabata. Idan har ya kasance baya motsa jikinsa ballantana ma har ya samu damar fitar da sikarin da bai da wani amfani a jikinsa,wato abubuwan da suke sinadarai a jikinsa.
To suma wadannan abubuwan da suka kasance bai samu fitar da su ba daga jikinsa,suna iya samar ma sa da yanayi ya ji kamar ya kamu da cutar ta ciwon sikari. Akwai kuma abu na hudu da ake kira idiofatic (dalilan ba za su baka dama ka gane karara ka gane yanayin) amma sai mutum ya rika jin alamu ne kamar ya kamu da ciwon sikari.Wadannan sune abubuwan da suke da nasaba da cutar diabetes a jikinka, sune kuma suka fi yin tasiri dangane da cutar sikari.Sai dai kuma shi diagnosis wato bincike akwai shi nau’i nau’i.
Wadanne hanyoyi za abi domin kaucewa kamuwa da cutar diabetes? Hanyoyin kaucewa kamuwa da cutar sikari shi ne na farko mutum ya rika zuiwa wurin neman shawararwari dangane da cutar a asbiti, ko kuma malaman kiwon lafiya domin su rika ankarar da shi kan yanayin ita cutar.
Na farko yadda mutum zai samu tsira daga kamuwa da cutar sikari. Na biyu kuma mutum ya rika kiyaye nau’in abincin da zai rika ci manufa anan nau’in abincin da zai rika ci shi ne, idan shekaru sun fara tafiya, sai a kiyaye da irin nau’in abincin da za a rika ci, amma ba kowanne nau’in abinci bane mutum zai ci. Misali wanda ya kunshi suga, sai kuma wanda aka tanadar da shi ta fuskar kimiyya,ya kasance mutum yana kiyayewa da hakan in dai har ka san da akwai suga ko kuma glucose to sai a yi kokarin kiyayewa saboda samun tsira daga nau’in abubuwan da suke haddasa ita cutar ciwon sikari.
Ana gadonsa amma baya tashi daga jikin wannan ya koma jikin wancan,amma ta bangaren jini akan gaje shi kamar yadda masana suka bayyana.Akwai kuma maganar kula da yawan motsa hiki saboda ya watsar da wasu nau’oin suga a jikinsa,daga shekara 25 zuwa 30 yakamata mutum ya fara tunanin irin nau’in abincin daya dace ya ci.
A gidan mutum ya dace da akwai irin abincin da za a rika dafawa, daga cikin nau’ukan abinci shida da ake da su, ya dace ka yi amfani da uku yau ka cid a safe daban, ba wai da safe ka ci nau’in abincin da yake kara kuzari ba,da rana kuma haka harzuwa yamma wannan ba haka ne ake so ba.Amma idan mai faruwa ta riga ta faru ai dole ne kuma aje a nemi magani.
Wacce hanya ce za a rika maganin ita cutar? Zaka iya magani ita cutar ba tare da ka je wurin malaman kiwon lafiya ba sun yi bincike sun san wanne irin nau’in ciwon suga da kake dauke da shi,kamar dai yadda aka dade da yin bayani akwai nau’i uku.Sun hada da defended, indefended da kuma Secondary wadannan sune nau’uka uku,saboda haka abu mafi dacewa shi ne aje wurin masana su yi bincike,su ma ba za su iya yin bayani ba,sai sun sa an yi bincike tukunna.