Cututtukan Da Ake Dauka Ta Hanyoyin Iska (4)  

Iska

A Wannan mako ma  za mu ci gaba da kawo maku hirar daga inda muka tsaya tare da Dokta Isa Abu Abdurrahaman Likita mai zaman kansa, kamar yadda ya yi bayanai kan cututtukan da ake dauka ta iska.

Idan har mutum ya kai shekara hamsin nau’in abincin da ya kunshi Protein ko ya ci shi, ba zai ma sa wani tasiri a jiki ba, sai dai ya rika gyara masa hasken jikinsa, hakanan kuma  ba za a samu bunkasa wani sinadarin Calcium, shi ma jini ana samunsa ne ta Protein, idan mutum har ya kai wadancan shekarun mutum bai kamata ba a ci gaba da ba shi abincin daya kunshi ba domin bargonsa ba zai ci gaba da ginuwa ba, sai dai kawai ba a ba shi saboda kare shi daga shigar wasu cututtuka.

Nau’o’in abincin wadanda suka kunshi Protein suna taimakawa wajen bunkasa su sinadaran da suke karewa da taimakawa jiki daga kamuwa daga cututtuka. Sai dai kuma wani al’amari  na daban shi ne cells wato wasu sinadarai da suke taka muhimmiyar rawa wajen tafiyar harkokin rayuwar mutum, saboda suna cikin sinadaran ne wadanda kuma akwai su wadanda suka kai milyoyi ana samar da su wasu kuma suna mutuwa.

Sinadaran suna samar da wasu nau’o’in jini biyu wato white blood cells da kuma red blood cells, manufa masu daukar iskar da  ake amfani da ita a jikin mutum mai suna Odygen, yayin da shi kuma shi WBC ko white bloo cells nau’in jinin masu kare jiki ne daga kamuwa da wata cuta.

Yaro daga wata daya har zuwa wata takwas dan jaririn ke nan kaga ai bai kai ga zama yaro ba, a lokacin bai fara iya daukar sautin wasu mutanen gidansu ba, ko kuma bai fara sanin su wanene ba, wannan daga wata takwas ne zai fa nazarin gane muryar mahaifiyarsa ya gane muryarta da kuma mutanen da  suke zaune kusa da shi wao ‘yan’uwansa da muryoyinsu.

To idan har wannan lokacin idan har yaro yana da sinadaran Plamadiosis  na Anopheles moskuito da ta cije shi, dalilin haka kuma har aka samu wasu cututtuka suka shiga jikin shi,  a sanadiyar haka har jikin na shi ya kai ga zafi mai yawa saboda yanayin zafi ko sanyin jikin mutum akwai mizanin da ya dace ace yana wurin, idan kuma har aka samu akasin haka to an hadu da matsala ,to idan har aka bar yaron nan zafi yai yawa, suka kai ga shiga cells din shi, to idan har ya wuce kima to ka san komai na yaro bai kai ga balaga ba, wato isa mizanin daya dace.

Su wadannan cells din za su lalace, saboda haka idan wani lokaci idan aka kawo nazarin kiwon lafiya  ko sha ka tafi ne, ko kuma babban asibiti  wanda ake kwantar da marasa lafaiya ne, ko wadanda suka  kware a kan harkar asibiti ne wato kwararru to dole ne sai sun bi ta wata hanya wadda ake koyar da Malaman kiwon lafiya kamar su  Unguwar-Zoma, Nurses, su je su nemi ruwa su sa a Towel su samu damar kwanar da yanayin jikin na shi yaron, ya koma  kamar yadda ya dace har a samu ba shi maganin Paracetamol ke nan.

Wannan ina maka maganar normal attack bom blast wannan yana karkashi Trauma ne, sai kuma na uku emotion shi ma yana kawo kawo sanadiyar kamuwa da wasu cututtuka. Ana nufin tunani kamar mutm na tunanin abinda yake fitar da shi daga cikin kangi, alal misali idan muna tare da kai ko wanne lokaci, ko dace ba zan baka wani abu ba, idan kana jin dadin zama da ni, da zarar an ce yau bani wani abu ya same ni sai ka ji wani abu a jikin ka.

 

 

Exit mobile version