Cututtukan Da Ake Dauka Ta Hanyoyin Iska (6)

iska

Coronavirus pneumonia. Conceptual computer illustration showing coronavirus in human lungs. Different strains of coronavirus are responsible for diseases such as the common cold, gastroenteritis and SARS (severe acute respiratory syndrome). A new coronavirus (SARS-CoV-2) emerged in Wuhan, China, in December 2019. The virus causes a mild respiratory illness (Covid-19) that can develop into pneumonia and be fatal in some cases. The coronaviruses take their name from their crown (corona) of surface proteins, which are used to attach and penetrate their host cells. Once inside the cells, the particles use the cells' machinery to make more copies of the virus.

wannan makon shi ne karshen hirar da muka yi da Dakta Isa Abu Abdurrahman, kan cututtukan da ake dauka ta hanyoyin iska. A mako mai zuwa za nu kawo muku wata sabuwar hirar.

Haka kuma al’amarin “communicable disease” ko cutar da take yaduwa musamman ta cudanya tsakanin wannan da wancan.

Idan kuma muka sake duba cutar da ake dauka tsakanin wane da wane, misali, Allah ya kyauta, muna aiki da kai da Hajiya, ya kasance kuma ni ina fama da cutar Tuberculin, ina tari ko da wane lokaci.

A nan kuma kuna iya kamuwa da ita cutar domin kuwa kullun muna yin hulda tare, ina tare da ku, wani abu daban, shi ne ku ba ku sa facemask ba, bugu da kari kuma ita cutar ta hanyar iska ce ake kamuwa da ita. Don kamar dai yadda aka sani ita cutar Tuberculin wato Tarinfuka, ana iya kamuwa da ita ta kai  tsaye ko ba ta kai tsaye ba.

 

Me ake nufi da alamu ko yanayin da ake shiga idan an kamu da cutar da ke dauka ta hanyar iska?

Abin da mutum ya lura da shi da idonsa daga wurin mara lafiya shi ake nufi da al’amar shigar cutar, saboda haka da zarar ka gani kashi dari, ko saba’in, yayin da shi symtom  kuma abin da shi wanda bai da lafiyar yake ji a jikinsa ne. Shi yasa su masu nazarin kiwon lafiya ko bincike a kansa suka ce ba su wadannan abubuwan biyu kadai ba ne za su iya bada dama ta daukar mataki kan irin yadda za a bullo ma ita cutar ba, idan maganar maganin ta ta taso.

Duk wannan ba za a iya daukar wani mataki ba, na yadda za a bada maganin, ko allura ce ta dace har sai lokacin da aka yi bincike kan fitsari da Kashi da yau da Jini da duk wadansu abubuwan da ake bukata tukunna. Don ka fada mani kana jin wani yanayi a jikinka ai wata cutar tana kama da wata, har sai an gudanar da bincike tukuna.

Sannan kuma zan iya sake ba ka dalilan da suke sa ana kamuwa da cutar da ake dauka ta iska wadanda su sinadaran ko kwayoyin cutar ba za ka iya ganinsu ba,

har sai an yi amfani da madubin Likita wanda ake kira da turanci microscope.

Da ita na’urar ake amfani domin ita ce za ta nuna yadda shi al’amarin na cutar yake. Kamar dai yadda Bature ya ce ba wata cutar al’amarin ba wani abu bane in banda yadda su kwayoyin cutar suke samun damar shiga. Abin kuma yana farawa ne daga lokacin da aka samu sign and symtom ganin yanayin da mara lafiya yake ciki, ko kuma yadda ya yi bayanin irin yadda yake ji a jikinsa.Isa

Exit mobile version