Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
Home KIWON LAFIYA

Cututtukan Da Shan Sigari Ke Haifarwa

by Muhammad
December 24, 2020
in KIWON LAFIYA
6 min read
Shan Sigari
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram

Yin amfani ko shan da taba ya kan haifar da cututtukan daji fiye da nau’oi goma. A duk lokacin da a ka shaki hayakin taba, akwai sinadarai masu guba wadanda suke kasancewa ga jiki. Daga yawancin sinadaran na taba, akalla nau’oi saba’in an gano cewar suna sanadiyar kamuwa da cutar daji. Masu shan taba suna cikin hadari mafi girma na kamuwa da cutar sankarar bargon kashi; da ciwon daji na hanci da kuma na sauran sassan cikin hanci; da hanji, da koda , da kuma hanta, da matsarmama , da ciki ko kuma ciwon daji na halittar da ke fitar da kwayoyin haihuwa na mata; da kuma ciwon daji na hanyoyin fitsari (ciki har da mafitsara, da kuma sauran jijiyoyin bangaren). Binciken da aka yi kwanan nan sun nuna cewar alakar shan taba da kuma karuwar hadarin samun ciwon daji na nono (8f), musamman ma mata masu shan taba da suka fara shan taba kafin su fara daukar ciki. Hakanan kuma shan taba na kara yiyuwar hadarin samun ciwon daji na mahaifaga matan (8g) da ke fama da su wadannan cututtuka na yawan karuwa ne tare da yawan tabar da kuma tsawon lokacin da a ka yi ana sha, saboda tsawon lokaci a na shan taba na sa jiki kamuwa da sinadarai wadanda suke da   guba. Shan taba mara hayaki na dauke da kwayoyin cuta har 28 wadanda suke haifar da ciwon daji na cikin baki da makogwaro da kuma matsarmama. Wani abu kuma wanda ba asani ba shi ne ci gaba da yin amfani da taba bayan an gano ciwon daji yana kara tsananta cutar, saboda da kuwa shi hayakin taba na iya canza kwayar halitta, wanda zai iya kara girman ciwon dajin; da kawo tangarka ga maganin ciwon daji; da kuma kara yawan matsalolin maganin.

 

samndaads

Mutuwar Dan Tayi:

Yin amfani da taba da kuma shakar hayakin taba a lokacin daukar ciki ga mace wannan ya na kara hadarin mutuwar dan tayin ciki wato abinda yake cikin mahaifa. Mata wadanda suke shan taba ko kuma suke shakar hayakin taba lokacin da suke renon ciki suna cikin hadarin zubewar cikin. Zubewar ciki (haihuwar tayin da ya mutu a cikin mahaifa) na faruwa ne a lokuta da yawa a sakamakon rashin isasshiyar ‘odygen’ wadda ake shaka da rashin dai-daiton mahaifa wanda iskar ‘carbon monodide’ke haifarwa daga hayakin taba da sinadarin ‘nicotine’ wanda yake cikin taba. Mata masu shan taba suna cikin hadarin samun ciki a wajen mahaifa, mai mummunan hadari ga mahaifiya, a nan yayin da ta ke reon cikin ya kan makale a wajen mahaifa. Saboda da haka ne, daina shan taba da kuma samun kariya daga shakar hayakin da mai shan taba ke fitarwa yana da mahimmanci ga mata masu haihuwa, ko kuma masu shirin daukar ciki da kuma lokacin renon renon shi cikin.

Hana Girman Dan Da Ke Cikin Mahaifa, Haihuwar Dan Wanda Ba Ya Da Cikakken Nauyi Da Wanda Bai Kai Wata Tara Ba:

Duk wani nau’i na amfani da taba ko kuma shiga cikin hayakin taba lokacin renon ciki zai iya zama abu mai illa ga lafiya da kuma girman dan tayin yaron da ke ciki. Yaran da aka haifa ga matan da suke shan taba, ko yin amfani da taba gari, ko kuma su ke shakar hayakin da mai shan taba yake fitarwa a lokacin da suke renon ciki suna da hadarin haihuwar bakwaini da kuma haihuwar yaron da nauyin sa bai cika ba. Yaran da aka haife su a bakwaini da kuma wadanda nauyin su bai cika ba na iya samun matsalolin rashi lafiyana tsawon rayuwar su, ciki har da samun cututtuka masu tsanani bayan sun girma.

 

Karancin Tunani/Mantuwa:

Shan taba wani abu ne wanda yake da hadarin lalata kwakwalwa, wanda wani rukuni na cututtuka ne wanda kan haifar da karancin tunanin mutum wanda kuma bashi da magani tabbatacce a halin yanzu. Karancin tunanin abu ne da ya ke habaka, ya kan shafi ƙwaƙwalwar mutum, da halayyar mutum da kuma kwarewa da tsayawa ga ayyukan yau da kullum. Baya ga abin da wannan ciwo ke haifarwa wajen hana mutum zarafin ayyuka, cutar zata iya zama mai nauyi kwarai ga iyali ko masu kulawa da mai cutar. Cutar ‘Alzheimer’mafi yawa a cikin irin wannan cututtuka, kuma an kiyasta kimanin kashi goma sha huhu (14) cikin dari (100) na cutar a duniya na da alaka da shan taba.

 

Raunin Mazakuta:

 

Mutuwar Jariri Farad-daya:

Mutuwar jarirai farat-daya (SIDS) ita ce mai faruwa kwatsam, ba tare da wani dalili da a ke iya gani ba ga yara‘yan kasa da shekara 1. An san cewa shan taba yayin goyon ciki na kara hadarin mutuwar farat-daya ga yara, kuma hadarin ya kan kara karuwa tare da bin ‘ya’yan da suka Haifa, kuma suka ci gaba da shan taba bayan haihuwar.

 

Jinin Haila Da Yankewar Haihuwa:

Mata wadanda suke shan taba zasu iya jinin haila/wata mai ciwo da kuma zafi da kuma samun alamomin yankewar haihuwa. Yankewar haihuwa ta kan faru cikin shekara daya zuwa hudu ga mata masu shan taba, kasa da lokacin da a ka sani saboda shan taba yana rage damar samar da kwan haihuwana mace, wanda ya kan haifar da rashin samun damar haihuwa da kuma karancin rowan halittar ‘estrogen’.

 

Haihuwar Yara Masu Lahanin Halittu:

Shan taba yana iya lalata kwayar halitta tare da lalata kwayar halitta ta gado (DNA), wanda hakan yake haifar da lahani ga halittar jariri. A wasu binciken ilimi an gano cewar mutanen da suke shan taba suna da hadarin haihuwar yaron\ wanda ke iya kamuwa da ciwon daji. Shan taba ga mace a farkon lokacin da ta ke renon ciki na kara mata yiyuwar hakarin haihuwar jariri mai yankakken lebe ko kuma baki. An kuma lura cewar mutanen da iyayensu suka sha taba a lokacin renonciki suna da ƙarancin yawan kwayar halitta fiye da maza wadanda iyayensu ba su taba shan taba ba.

 

Rashin Gani:

 

Raunin Kashi:

Iskar ‘Carbon monodide’ da ta ke cikin hayakin taba, babbar guba ce irin wacce a ke samu a hayakin mota, ta kan danfara zuwa ga ‘hemoglobin’na cikin jini cikin sauki fiye da iskar ‘odygen’ da jiki yake bukata, don haka ne sai ta rage zuwan iskar odygen zuwa jikin mutum. Masu shan taba sun fi saukin samun raunin kashi, yadda karfin kashin ke raguwa da saukin karyewa.Idan kuma suka fuskanci matsalolin a kashi, akwai jinjiri ko rashin samun nasarar warkewa.

 

SendShareTweetShare
Previous Post

An Daure Dillalan Gidaje Na Bogi Shekara Uku A Abuja

Next Post

Fyade Da Hanyoyin Magance Shi Ta Fuskar Nazari

RelatedPosts

Magani

Cutar Da Ba Ta Jin Magani Ta Bulla

by Muhammad
22 hours ago
0

Kwararru al’amarin daya shafi kiwon lafiyar al’umma sun yi gargadin...

Baure

Amfani 15 Na Baure Ga Lafiyar Dan Adam

by Muhammad
22 hours ago
0

Tsawon shekaru masu yawa da ska wuce, 'Baure wani nau'i...

Warin Baki

Abubuwa Tara Da Suke Sa Warin Baki Da Yadde Ake Kauce Musu

by Muhammad
5 days ago
0

Cikin ko wanne lungu da kuma sako na fadin duniya,...

Next Post
Fyade

Fyade Da Hanyoyin Magance Shi Ta Fuskar Nazari

Domin sanya talla ko karin bayani a tuntube wannan numbar +2348126152609.

Leadership Epaper
ADVERTISEMENT
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us

© 2020 Leadership Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2020 Leadership Group .

Go to mobile version