Cuwa-cuwar Fitar Da Doya Waje: Majalisa Za Ta Tuhumi Audu Ogbeh

Daga Mustapha Hamid, Abuja

A jiya, Majalisar Wakilai ta tarayya ta umurci kwamitocin majalisar da ke kula da harkar noma, gudanarwa, Kwastam da su tuhumi ministan noma, Audu Ogbeh bisa ƙememen da yayi ga dokar hana fitar da doya waje.

Cikin waɗanda majalisar ta aike wad a sammaci akwai Shugaban Hukumar Kwastam, Kanar Hameed Ali; Babban Daraktan Cibiyar Inganta Fita da Kaya Waje, Mista Olusegun Awolowo, Darakta Janar na Hukumar Kula Da Inganci Ta Ƙasa, Mista Osita Aboloma da wasu shugabannin cibiyoyi da hukumomi domin su yi bayanin dalilin da ya sa suka sakar wa Ministan marar aikata wannan aiki ba bisa ƙa’ida ba.

Wannan tuhuma ta biyo bayan wani ƙorafi da Honorabul Gaza Jonathan Ghefƙi ya kawo, mai taken, “Buƙatuwar bin diddigin wasu kayayyakin abinci da aka fitar da su daga Nijeriya ba bisa ƙa’ida ba, kuma waɗanda suke da ƙarancin inganci.”

A yayin da yake gabatar da ƙorafin a gaban majalisa, Honorabul Gaza ya ce; “Kwanan nan aka samu rahoto da ke bayyana cewa an fita da Tan 72 na doya a lokutan baya cikin watan Yunin 2017, wanda kuma ƙasar Amurka ta ƙi amsar su, saboda kafin su ƙara so har sun fara lalace wa. Al’amarin da ya janyo wa Nijeriya abin kunya, ta yadda har an fara zargin Nijeriya da fitar da kayan jabu.

“A ƙoƙarin da gwamnatin Nijeriya ke yi na samar da wasu hanyoyin dogaro da kai da samar da kuɗaɗen shiga, wanda kuma har da fitar da kamfanin gona. Bisa wannan dalilin ne gwamnatin tarayya ta ƙaddamar da shirin fitar da doya wanda aka ayyana cewa nan da shekaru huɗu za a samu ribar dalar amurka 10.

“Dokar  ta lissafo jerin wasu daga cikin amfanin gonan da aka haramta fitar dasu daga Nijeriya, waɗanda suka haɗa da Wake, Rogo, Masara, Shinkafa, Doya da sauransu.” Inji Ɗan majalisar

Wannan tuhuma dai tuni aka tattauna ta, bisa jagorancin Kakakin Majalisar Wakilai, Yakubu Dogara.

Exit mobile version