Daga Suleiman Ibrahim
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da nadin DIG Usman Alkali Baba a matsayin mukaddashin sufeto janar na ‘yan sanda.
Nan take ya maye gurbin Mohammed Abubakar Adamu.
Ministan harkokin ‘yan sanda, Maigari Dingyadi ne ya bayyana hakan ga manema labarai na fadar gwamnati a ranar Talata.
In ba a manta ba, a ranar 4 ga watan Fabrairu ne, shugaba Buhari ya tsawaita wa’adin Mohammed Adamu a matsayin Sufeto Janar na ’yan sanda na tsawon watanni uku inda daga nan tsohon shugaban ‘yan sandan ya kwashe watanni biyu da kwana uku.
A cewar ministan, nadin Baba an yi shi ne a nazarce, bayan shugaba buhari ya yi la’akari da batutuwan kwarewa, can-canta da kuma samun shekaru masu yawa a aikin.