Da ɗimi-ɗiminsa: Tsohon Ɗantakarar Shugaban Ƙasa Bashir Tofa Ya Rasu

Daga Abdullahi Muhammad Sheka, Kano

Rahotanni daga birnin Kano  na cewa tsohon ɗantakarar shugaban Nijeriya Alhaji Bashir Othman Tofa ya rasu.
Ya rasu ne da asubahin Litinin ɗin nan a asibitin Malam Aminu Kano, yana da shekara 74 a duniya.

Wasu makusantansa sun tabbatar da cewa tsohon ɗansiyasar ya yi fama da jinya.
A makon jiya ne aka yi ta watsa labarin da ke cewa Bashir Tofa ya rasu, amma daga bisani aka tabbatar bai rasu ba.

Wasu majiyoyi sun ce za a yi jana’izarsa a gidansa da ke unguwar Gandun Albasa a birnin Kano.
Alhaji Bashir Tofa, wanda fitaccen ɗankasuwa ne kuma marubuci, ya bar mata da ‘ya’ya da dama.

Marigayin ya tsunduma harkokin siyasa a shekarar 1976 inda ya zama kansila a karamar hukumar Dawakin Tofa a 1977.
Tun daga wancan lokacin ya riƙe muƙamai da dama na siyasa ciki har da Sakataren jam’iyyar National Party of Nigeria, NPN reshen Jihar Kano.

Bashir Othman Tofa ya tsaya takarar shugaban Nijeriya a ƙarƙashin rusasshiyar jam’iyyar National Republican Convention, NRC, a zaven da aka gudanar ranar 12 ga watan Yuni na shekarar 1993 tsakaninsa da marigayi Chief Moshood Kashimawo Olawale Abiola ko MKO Abiola (a takaice) na rusasshiyar jam’iyyar Social Democratic Party, SDP.

Exit mobile version