Hukumar yaki da cin hanci da rashawa da sauraron korafe-korafen jama’a ta jihar Kano ta shigar da sabbin tuhume-tuhume kan almundahana a kan tsohon gwamnan jihar Dr. Abdullahi Ganduje.
Shugaban Hukumar, Muhuyi Magaji ne ya bayyana hakan a shirin ‘Sunrise Daily’ na gidan talabijin na Channels a ranar Talata, inda ya zargi gwamnatin Ganduje da karkatar da kudaden al’umma.
- Bukukuwan Sallah: Rundunar ‘Yansanda Ta Kama Bata-gari 104 Da Ake Zargi Da Aikata Laifuka A Kano
- Hawan Daushe: ‘Yansanda Sun Cafke ‘Yan Daba 54 A Kano
Ya bayyana cewa, bincike ya nuna yadda aka karkatar da naira biliyan 51.3 na kudaden kananan hukumomi zuwa wasu asusun ajiya da basu da hurumin karbar irin wadannan kudaden.
A cewar Muhuyi, gwamnatin Ganduje na cire naira biliyan 1 a duk wata daga asusun jihar ba bisa ka’ida ba.
Ya kuma yi ikirarin cewa, an zuba Naira biliyan 4 ga asusun wani kamfanin noma daga asusun tattara harajin jihar ba tare da wani dalili ba.