Tattalin arzikin Nijeriya ya nuna juriya da kuma ci gaba, bisa ga kididdigar da hukumar kididdiga ta kasa ta fitar, wanda ya nuna cewa, tattalin arzikin cikin gida (GDP) ya karu da kashi 4.23% a rubu’i na biyu na shekarar 2025.
Hakan ya nuna ci gaba akan abunda aka samu na 3.48% a kwata na biyu na 2025 da 3.13% da aka samu a kwatan farko na 2025.
Ɓangaren noma ya karu zuwa kashi 2.82%, saɓanin yadda yake 2.60% a daidai irin wannan zango na 2024.