Da Dimi-dimi: An Tabbatar Da Bullar Sabuwar Cutar Korona A Nijeriya

Cutar Ta Bulla Ta Hanyar Fasinjoji Biyu Daga Afirka Ta Kudu

Daga Sulaiman Ibrahim,

Cibiyar Kula da Cututtuka ta Nijeriya a safiyar Laraba ta tabbatar da bullar cutar Omicron (sabuwar nau’in cutar korona) ta farko a kasar.

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da cibiyar ta fitar mai dauke da sa hannun Darakta Janar, Dr Ifedayo Adetifa.

An ba da rahoton cewa Omicron sabon nau’in cutar coronavirus ce, Afirka ta Kudu ce ta ba da rahoton kuma an fara gano ta a Botswana.

Bayan gano hakan, kasashe irin su Birtaniya, Saudiya, Isra’ila da dai sauransu sun sanya dokar hana zirga-zirga a kasashen kudancin Afirka.

Hakazalika, gwamnatin Canada ta kuma bayyana cewa ta gano wasu fasinjoji biyu dauke da cutar daga Nijeriya. Gwamnatin tarayya ta hannun kwamitin shugaban kasa kan COVID-19, ta ce tana gudanar da bincike kan lamarin domin samun karin bayani.

Yadda sanarwar ta kasance, “A bisa tsarin gwajin tafiye-tafiye na yau da kullun da ake bukata ga dukkan matafiya na kasa da kasa, bin diddigin kwayoyin halitta a Cibiyar Kula da Cututtuka ta Nijeriya ta dakin gwaje-gwajenta na National Reference Laboratory, Abuja, ya tabbatar da bullar cutar sabuwar korona Wacce ake Kira Omicron ta farko a Nijeriya.”

Exit mobile version