Sanata Ahmad Lawan na jam’iyyar APC mai mulki ne ya lashe zaben shugabancin majalisar dattawan Nijeriya, sashe na 9. Shekarun Ahmad Lawan 60, ya na wakiltar Yobe ta arewa ne a majalisar dattawan Nijeriya, an fara zaben shi a matsayin sanata ne a shekarar 2007.
A wannan karon Lawan Ahmad ya samu nasarar zama shugaban majalisar dattawan ne bayan da ya samu kuri’a 79 daga cikin 107 na ‘yan majalisar dattawa da suka kada kuri’a.
A biyo mu don samun cikakkun labarai…