Da Dimi-Diminsa: Ahmad Lawan Ya Zama Shugaban Majalisar Dattawa

Sanata Ahmad Lawan na jam’iyyar APC mai mulki ne ya lashe zaben shugabancin majalisar dattawan Nijeriya, sashe na 9. Shekarun Ahmad Lawan 60, ya na wakiltar Yobe ta arewa ne a majalisar dattawan Nijeriya, an fara zaben shi a matsayin sanata ne a shekarar 2007.

A wannan karon Lawan Ahmad ya samu nasarar zama shugaban majalisar dattawan ne bayan da ya samu kuri’a 79 daga cikin 107 na ‘yan majalisar dattawa da suka kada kuri’a.

A biyo mu don samun cikakkun labarai

Exit mobile version