A yau ne Kungiyar Malaman Jami’a ta Nijeriya ASUU ta amince cewa za janye yajin aikin da take tsaka da yi.
Kungiyar ASUU dai ta kwashe watanni takwas tana wannan yajin aiki.
Kungiyar Malaman Jami’o’in ta cimma wannan matsaya ta janye yajin aiki ne bayan kammala wani zaman musamman da ta yi da wakilan gwamnati wanda ministan kwadago, Dr. Chris Ngige ya jagoranta.
Gwamnatin Buhari ta ce za ta ba malaman bayar da Naira Biliyan 70 ga Malaman Jami’an, wanda wannan ya sa malaman suka yi niyyar janye yajin aikin.